A maimakon daukaka kara, kamata ya yi PDP ta nemi afuwan 'yan Najeriya - Lai Mohammed

A maimakon daukaka kara, kamata ya yi PDP ta nemi afuwan 'yan Najeriya - Lai Mohammed

Ministan Yada Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed ya bukaci jam'iyyar PDP da dan takarar shugaban kasarta a zaben da ya gabata su nemi afuwar 'yan Najeriya kan 'bata lokacin' gwamnatin Buhari game da batun karar zabe.

Channels Tv ta ruwaito cewa Mr Lai Mohammed ya ce a maimakon daukaka kara kan hukuncin da Kotun sauraron karrakin zaben shugaban kasa ta yanke a ranar Laraba, kamata ya yi jam'iyyar adawar ta nemi afuwar 'yan Najeriya saboda yunkurin da su kayi na bata wa gwamnati lokaci.

A sanarwar da ya fitar a St Petersburg na kasar Rasha a ranar Alhamis, Ministan ya ce duk da cewa PDP da dan takarar ta suna da damar daukaka kara kan shari'ar zai fi zama alheri idan sun farga daga mafarkin da suke yi.

DUBA WANNAN: Wani mutum da ya yi sojan gona a matsayin CP ya damfari sanatan arewa N1.8m

Mohammed ya ce, "'Yan Najeriya sun gaji da hayaniya kuma za su so da jam'iyyar hamayyar da su ka sha kaye a akwatin zabe da kotu su hada hannu da gwamnati domin kawo cigaba a Najeriya.

"Hakan zai fa zama alheri duba da cewa alkalan sun hada kai wurin tabbatar da nasarar Shugaba Buhari kuma sunyi watsi da dukkan korafe-korafen da jam'iyyar adawar suka gabatar inda suka jadada cewa shugaban kasa ya cancanci tsayawa takarar."

Alhaji Mohammed ya ce kamata ya yi jam'iyyar PDP da dan takarar shugaban kasarta su gode wa Allah da ba a ayi kararsu a kotu ba saboda gabatar da hujjojin da suka samo ta haramtattun hanya a maimakon neman muzanta fannin shari'a.

Ministan ya kuma mika godiyarsa ga 'yan Najeriya dda suka zabe Shugaba Buhari tare da neman goyon bayansu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel