Masana sun gargadi wasu Gwamnonin arewa a kan wani mataki da suka dauka

Masana sun gargadi wasu Gwamnonin arewa a kan wani mataki da suka dauka

Tsananin son samo mafita akan rashin tsaro a jiharsa, Gwamnan jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari a makon da ya gabata yayi wani abu da ba a yi tsammani ba.

Shi tare da sauran manyan jami’an gwamnati, jami’an tsaro, sarakunan gargajiya da wakilan Miyetti Allah, sun yi wata ganawa tare da wakilan kungiyar yan bindigar da suka addabi jiharsa.

“Mun shirya yin sulhu da yan bindiga kuma a shirye muke mu je duk inda suka gayyace mu. Don haka bama tsoron ganawa da kowa domin kawo karshen wannan matsalar.” inji Masari.

A wani taron kuma Masari ya fada ma shugabannin yan ta’addan cewa “Shugaban kasa ya shawarce mu da muyi Magana da ku. Kuma mun yi.”

Jihar Katsina na cikin wani mawuacin hali. Haka ma jihohin Zamffara da Katsina a yankin arewa maso yammacin kasar wadanda ke raba iyakoki da Katsina. Yan bindiga na ta kai masu hare-hare, fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma masu fashin shanu. Yankin arewa maso yamma da a farko aka kare daga mummunan hare-haren Boko Haram da ke arewa maso gabas, ya zama wani babban dandamali na rikici.

Don haka a kokarinsu na zakuwa waje son dawo da tsaro a jihohinsu, gwamonin arewa maso yamma sun shiga yarjejeniyar alkawari tare da yan bindigar da kuma basu shirin afuwa, wanda ba a bayyana ba.

Amma dai gwamnoin sun amince da cewar a kokarin kawo zaman lafiya, yan bindigan su ajiye makamansu. “Daga yau, kada wata kungiyar yan banga ko kungiyar sa kai wa kowani makiyaya hari ko su kashe shi, domin ya zama dole ayi sadaukarwa daga bangarorin biyu domin wanzar da zaman lafiya,” inji yarjejeniyar.

Sannan kuma an ba yan bindigar dammar ajiye makamnsu yayin sakin mutanen da suka yi garkuwa da su.

Bello Matawalle, gwamnan jihar Zamfara yace: “Gwamnonin sun dauki mataki iri guda, kuma ku dauki mataki iri guda don kada ku sace dabbobi, garkuwa ko kashe wani.”

Babbar sakatariyar din-din-din na ma’aikatar ayyuka na musamman, ofisi sakataren gwamnatin tarayya, Dr Amina Shamaki ta yaba da kokarin, inda tayi sharhin cewa ya kamata jihohin da ke fuskantar matsalolin tsaro su yi koyi da shirin sulhu na Matawalle.

KU KARANTA KUMA: IRT sun kama gagararren jagoran yan bindiga da ya sace mutane 50 a Kaduna

A takarda, babu shakka anga cewa yan bindigan sun bayar da hadin kai. Amma wani tabacci ake dashi cewa ba za su bijire ba? Shin wata kungiya da bata bisa doka za ta iya riko da yarjejeniya? Za a iya yarda da kalaman bakinsu? Shin takarda da aka baiwa wasu yan ta’adda da aka sani zai iya kawo karshen rikici? Masari da kansa ne a yan lokuta da suka gabata yace rikon yan bindiga karshe ne. “Idan ka kashe mutum guda, wani zai fito saboda basu san darajar rai ba saboda rashin ilimi.”

“A gare mu, kalubalen babba ne. Tare da sama da kaso 60 na matasa marasa aikin yi, bakin hadarin ba zai kau ba sannan shirin afuwan zai kawo dan kwanciyar hankali kadan ne. Ya zama dole mahukunta su nemi mafita mai dorewa maimakon shiga yarjejeniya da yan ta’adda.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel