Jirgin ‘Yan Najeriya da ya fara tattaro wadanda ke kasar Afrika ta Kudu ya taba kasa

Jirgin ‘Yan Najeriya da ya fara tattaro wadanda ke kasar Afrika ta Kudu ya taba kasa

- Wannan ne jirgin farko na mutanen Najeriya da su ka dawo gida yanzu

- ‘Yan Najeriyar da ke cira ni a kasar Afrikan sun ji tsoron a hallaka su

- Harin da ake kai wa bakin haure ya sa jama’a ke barin Afrika ta Kudu

Jirgin ‘Yan Najeriya da ya fara tattaro wadanda ke kasar Afrika ta Kudu ya taba kasa

Hotunan wasu ‘Yan Najeriya da su ka bar Afrika ta Kudu
Source: UGC

Mu na da labari cewa jirgin farko da ke dauke da ‘yan Najeriya daga Afrika ta Kudu ya taba kasa a filin jirgin sama. ‘Yan Najeriyar sun baro kasar wajen ne saboda hare-haren da ake kai masu.

Idan ba ku manta ba, mutanen kasar Afrika ta Kudu su na kai wa bakin haure hari a cikin ‘yan kwanakin nan. Wannan ya sa wasu daga cikin ‘Yan Najeriya su ka bi jirgin Air Peace su ka tsero.

Jirgin farko da ya dauko ‘yan Najeriyar da su ka dawo gida don ganin damarsu sun iso Najeriya. Bakin sun dura cikin filin jirgin sama ne da kimanin karfe 11:00 na daren Ranar Larabar nan.

KU KARANTA: Gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta hana a dawo da wasu 'Yan Najeriya

Jirgin ‘Yan Najeriya da ya fara tattaro wadanda ke kasar Afrika ta Kudu ya taba kasa

Hotunan wasu ‘Yan Najeriya da su ka bar Afrika ta Kudu a jirgin Air Peace
Source: UGC

Wannan karo Masu ci ranin daga Najeriya sun gujewa munanan hare-haren da aka dade ana kai wa wadanda ba ‘yan kasa ba, sun dawo gida bayan sun samu jirgin da zai rage masu hanya.

‘Yan jarida da jami’an gwamnati su na filin jirgin lokacin da ‘yan kasar su ka dawo. Shugabar hukumar ‘Yan Najeriya da ke zaune a ketare, Abike Dabiri ce ta tarbi wadannan masu dawowar.

Abike Dabiri ta karbe su ne a madadin gwamnatin Najeriya inda Legit.ng ta dauki rohoto da hotuna. An ga wasu cikin fasinjojin jirgin wayam ba tare da sun dauko komai daga kasar ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel