Sama da mutane 800 ne suka nuna bukatar takarar zaben da za a yi a jihar Kebbi

Sama da mutane 800 ne suka nuna bukatar takarar zaben da za a yi a jihar Kebbi

- Sama da mutane 800 ne suka nuna bukatar takarar zaben kananan hukumomi da gunduma a jihar Kebbi karkashin jam'iyyar APC

- Mai magana da yawun jam'iyyar, Alhaji Sani Dododo ya sanar da hakan ga manema labarai

- Mutane 300 daga ciki ne suka nuna bukatar takarar shuwagabannin kananan hukumomi

Fiye da mutane 800 ne suka nuna bukatar takarar zaben kananan hukumomj karkashin jam'iyyar APC.

Akwai kananan hukumomi 21 da kuma gundumomi 225 a jihar ta Kebbi.

Mai magana da yawun jam'iyyar a jihar, Alhaji Sani Dododo, ya sanar da hakan ga manema labarai a Birnin Kebbi. Ya sanar da yadda mutane suka nuna bukatar takarar zaben da za a yi a ranar 26 ga watan Octoba na shekarar nan.

KU KARANTA: Tashin hankali: Dalibi na biyu ya rasa ransa sakamakon harbin 'yan sanda a Jami'ar Ekiti

Yace 300 daga ciki sun nuna bukatar takarar shugabancin kananan hukumomi, sai 500 daga ciki sun nuna bukatar takarar shugabancin gundumomi.

Dododo yace a cikin kananan hukumomin jihar 21, Birnin Kebbi ce ke da mafi yawan 'yan takarar.

Ya kara da cewa, Jam'iyyar ta raba jihar zuwa yankuna 6 inda ta shirya kwamiti 6 don duba yankunan.

"A shirye muke don kare bukata da wanzar da zaman lafiya a jam'iyyar."

Mai magana da yawun jam'iyyar yace, "za a baiwa kowanne Dan takara dama."

"Mun gano cewa wasu 'yan takarar na nunawa magoya bayansu takardar shaidar cewa jam'iyyar tana goyon bayansu. Wannan ba gaskiya bane," ya ja kunne.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel