Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fidda naira biliyan 182 don gyara da yin sabbin tituna

Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fidda naira biliyan 182 don gyara da yin sabbin tituna

- Taron sabuwar majalisar zartarwa ta kasa na farko ya fara da gyara da yin tituna a fadin kasar nan

- Taron da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a jiya ya aminta da fidda Naira biliyan 182 don gyara da yin tituna

- Gyaran da yin sabbin titunan sun taba kusan duk sassa na kasar nan

A ranar Laraba ne majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fitarda Naira biliyan 182 don gyara da kuma yin sabbin tituna a fadin kasar nan.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci taron majalisar.

Karamin ministan aiyuka da gidaje, Alhaji Abubakar Aliyu, ya sanar da hakan ga manema labarai bayan taron farko da sabuwar majalisar ta yi a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Ya bayyana cewa kashin farko na aikin titin Legas zuwa Badagry ne da zai danganta zuwa iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin. Aikin zai ci Naira biliyan 15.2.

Ministan ya bayyana cewa majalisar ta amince da fitar da Naira biliyan 189 don yin tituna 14 a sassa daban-daban na fadin kasar nan.

KU KARANTA: Kudin makaranta 'ya'yana ya sa na fara garkuwa da mutane

"Mun amince da bada kwangilar aikin tituna 14 a fadin kasar nan. Sun hada da yin gadar Kontagora zuwa Rijau wanda zai ci Naira biliyan 1.12 sai kuma karin titi a hanyar Kano zuwa Katsina wanda zai ci Naira biliyan 9.4, " inji shi.

Kamar yadda ya sanar, titin Kontagora zuwa Bangi zai ci Naira biliyan 20.3 inda zai dauki watanni 48 domin kammalar aikin. Sai gyaran titin sansanin Marina zuwa Bonny da gadar Eko zai ci Naira biliyan 9.2 wanda za a kammala cikin shekara daya.

"Sauran titunan da za a gyara sun hada da titin yammavin Ibori zuwa Idomi a jihar Edo wanda zai ci Naira biliyan 4.5 kuma zai kammala cikin shekara daya; Yin titin Ilogu zuwa Ireni a jihohin Kwara da Osun zai lashe Naira biliyan 18.41," ya kara.

Ministan ya cigaba da fadin yadda majalisar ta amince da fidda Naira biliyan 2.5 don yin gadar Wudil da ke kan titin Kano zuwa Maiduguri da kuma Naira biliyan 12.3 don gyaran titin Wukari zuwa Ibi a jihar Taraba.

Ya kara da cewa majalisar ta amince da fidda Naira biliyan 10.6 don yin titin tashar jirgin ruwa ta Baro a jihar Niger, Naira biliyan 25 don gyaran titin Ajingi zuwa Kafin Hausa a jihar Jigawa sai kuma gyaran titin Abba zuwa Owerri da zai ci naira biliyan 6.98.

Hakazalika majalisar ta aminta da fitar da Naira biliyan 16.9 don gyaran titin Kaliyari zuwa Damaturu a jihar Yobe; Naira biliyan 17.3 don yin titin Yaba zuwa Yangoji a babban birnin tarayya da kuma Naira biliyan 12.7 don gyaran titin Nnnewi zuwa Okigwe a jihohin Imo da Anambra.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel