Babu ranar bude iyakokin kasar nan, inji shugaban kwastam na kasa

Babu ranar bude iyakokin kasar nan, inji shugaban kwastam na kasa

- Shugaban kwastam na kasa, Col. Hameed Ali mai ritaya ya kai ziyara garin Maigatari na jihar Katsina

- A ziyarar ta sa ne ya bayyana cewa babu ranar bude iyakokin kasar nan

- Ya sanar cewa har sai lokacin da kasashen da ke da makwaftaka da Najeriya sun aminta da dokokin habaka tattalin arzikin kasar nan

Shugaban hukumar kwastam ta kasa, Col. Hameed Ali mai ritaya, yace za a cigaba da garkame iyakokin Najeriya har sai kasashen da ke da iyaka da kasar sun aminta da dokokin gwamnatin Najeriya.

Shugaban ya sanar da hakan ne yayin da ya kai ziyara Maigatari, iyakar Nigeria da jamhuriyar Niger a ranar Laraba.

Yace Najeriya ba zata kalmashe kafafu tana kallon makwaftanta suna jibgo abubuwan da zasu cutar da tattalin arzikinta ba.

Ali, wanda ya isa Maigatari a jirgin sama, ya sanar da manema labarai cewa kasashen da ke makwaftaka da Najeriya na tallafawa wajen shigo da duk ababen da Najeriya ta haramta wadanda zasu iya kawo zagon kasa ga cigaban kasar.

Yace duk da matakin nan, kofa bude take domin tattaunawa akan sabbin yarjejeniyar da zasu mutunta dokokin tattalin arzikin kasar nan.

KU KARANTA: Musayan fursunoni: Yayinda gwamnatin Katsina ta saki yan bindiga 6, su kuma sun saki mutane 20 sa suka sace

Ya ce ziyararsa na daga cikin umarnin shugaban kasa. Shugaban kasar ya bukacesa da ya je ya gani da idonsa cigaban da aka samu tun lokacin da aka rufe iyakokin kasar nan.

Shugaban hukumar kwastam din ya bukaci jami'an hadin guiwar da ke iyakar da su tabbatar da rufe iyakar ba tare da yin wani abu da yaci karo da bukatar kasar ba.

Ya kara da cewa ziyararsa tazo da nufin duba walwalar jami'an tare da kawo hanyayin kara musu karfin guiwa.

"Za a cigaba da rufe iyakokin kasar nan har sai kasashen da ke da iyaka da Najeriya sun aminta da dokokin tattalin arzikin kasar nan ta shimfida, na game da abubuwan da ke shigowa kasar nan."

"Wannan ne lokaci na farko a tarihin kasar nan da aka hada jami'an hadin guiwa da suka kunshi Sojoji, kwastam da 'yan sanda duk a iyakokin kasar. Gwamnatin tarayya ta kirkiro hakan ne don tabbatar da rufewar iyakokin." Inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel