Patrick Lumumbu: Ana ganin masu cin haram da daraja a Najeriya

Patrick Lumumbu: Ana ganin masu cin haram da daraja a Najeriya

Tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa a kasar Kenya, Farfesa Patrick Lumumba, ya yi bayani game da abin da ya sa har yanzu rashin gaskiya yake samun gindin zama.

A ta bakin Patrick Lumumba, har yanzu ‘Yan kasar ba su gaji da wannan mugun aiki ba ne don haka aka gaza kawo karshensa. Farfesan yake cewa a irinsu Najeriya, ana girmama Barayi.

Shehin Malamin na kasar Kenya yace ba za a ga karshen satar dukiyar al’umma a duk kasar da ta ke ganin martaba da mutuncin wadanda su ka tara dukiya ta hanyar sata da rashin gaskiya ba.

Patrick Lumumba ya yi wannan jawabi ne wajen wani babban taron kungiyar ICAN ta manyan Akawun Najeriya da aka shirya Ranar Talata, 10 ga Watan Satumba, 2019 inda aka gayyacesa.

Ga kadan daga cikin abin da Malamin yake fada wajen wannan taro na 49 da ICAN ta shirya:

KU KARANTA: Za a daina rubuta jarrabawa a kan takardu a Jihar Kaduna

“Satar dikiyar kasa laifi ne ga Bil Adama. Tarihi ya nuna cewa muddin jama’a su ka gaji da rashin gaskiya a kasa, za su tashi tsaye. Kamar yadda Rumawa su kayi.”

“Aikin gina kasa nauyi ne da ya rataya kan kowa. Idan kai Akawu ne a ofis, dole ka yi aikin ka da kyau ta hanyar rike amana da tabbatar da cewa ka rike gaskiya.”

“Wani lokaci ne ina ganin cewa Najeriya da sauran ‘Yan Afrika ba su gaji da sata bane. Domin duk lokacin da su ka fara gajiya, abubuwa za su fara canzawa.”

Mukaddashin shugaban hukumar EFCC na Najeriya, Ibrahim Magu, ya halarci wannan taro inda ya nemi ICAN ta kirkiro kwas na musamman da za su horar da Akawu wajen yin gaskiya a aiki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel