Akwa Ibom: Sanata Ekpenyong ya Godswill doke Akpabio a kotun zabe

Akwa Ibom: Sanata Ekpenyong ya Godswill doke Akpabio a kotun zabe

Alkalan kotun da ke sauraron karar zaben da aka yi a jihar Akwa Ibom a zaben 2019 sun yi waje da karar da Sanata Godswill Akpabio inda yake kalubalantar kujerar Sanata Chris Ekpenyong.

Kotun da ke sauraron karar zaben da ke zama a Garin Uyo, ya tabbatar da nasarar da ‘dan takarar PDP, ya samu a zaben kujerar ‘dan majalisar dattawa na Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma.

A Ranar 11 ga Watan Satumba, 2019, Alkalai su ka ba Chris Ekpenyong gaskiya a shari’ar da ake yi tsakaninsa da tsohon Sanata Godswill Akpabio wanda ya wakilci yankin a majalisa ta takwas.

Kotu ta yi watsi da duk karar da Lauyoyin Godswill Akpabio su ka shigar inda su ka ce masu korafin ba su da gamsassun hujjoji masu karfi da za a iya yin la’akari da su wajen soke zaben.

Alkalin da ya yanke hukunci ya bayyana cewa ban da rashin hujjoji masu tsoka, mai korafin bai bi ka’idoji da sharudan gabatar da kara ba. An kuma zargi Akpabio da gaza kawo shaidu a kotu.

KU KARANTA: Alkalai sun yi watsi da karar Atiku a shari'arsa da Buhari

Godswill Akpabio ya dumfari kotu yana karar cewa Abokin takararsa na jam’iyyar PDP, bai samu mafi yawan halatattun kuri’un da aka kada ba, sannan ya ce zaben na sa ya sabawa ka’ida da dokar kasa.

Alkalai biyu cikin ukun da su ka saurari wannan kara sun tabbatar da cewa babu shakka Chris Ekpenyong shi ne zababben Sanatan Akwa Ibom na Arewa ta Yamma, kuma ba a saba doka a zaben ba.

Sai dai wani Alkali guda ya sabawa wannan hukunci da ‘yan uwansa su kayi. Amma mafi rinjayen hukuncin shi ne PDP ce ta lashe zabe. Tuni dai tsohon gwamnan ya zama Minista a Najeriya.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel