Ya guntule hannun makwabcinsa da adda, ya cika wandonsa da iska

Ya guntule hannun makwabcinsa da adda, ya cika wandonsa da iska

Wani matashi dan wiwi, Mustapha Adamu ya guntule hannun wani makwabcinsa mai suna Adamu Mohammed, ta hanyar amfani da adda wajen sare hannun yayin da wata takaddama ta shiga tsakaninsu, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan lamari ya auku ne a Unguwar Gede dake cikin garin Gwagwalada na babban birnin tarayya Abuja, kamar yadda wani mazaunin unguwar, Ibrahim Salihu ya tabbatar.

KU KARANTA: IRT sun kama gagararren jagoran yan bindiga da ya sace mutane 50 a Kaduna

Salihu yace wannan rikici ya auku ne a makon data gabata sakamakon wani sa’insa da aka samu tsakanin Adamu Muhammad da aka sare ma hannu da wasu gungun matasa yan wiwi a Unguwar Gede.

A cewar Salihu, rikicin ya samo asali ne a daidai lokacin da Adamu Muhammad ya gargadi matasan da su daina shan tabar wiwi a unguwar Gede, ashe wannan gargadi bai yi ma matasan dadi ba, inda suka fara dambe da shi.

“Daga wannan shawarar ne sai matasan suka fara fada da shi, amma Adamu Muhammad ya doki guda daga cikin matasan da icce a kai, inda shi kuma nan take Mustapha ya zaro adda daga cikin rigarsa ya cizge ma Adamu hannu.

“Ganin haka yasa jama’a suka taru da nufin kama Mustapha don mikashi ga Yansanda, amma zakara ya bashi sa’a ya ranta ana kare, kuma ya tsere.” Inji shi.

Majiyarmu ta ruwaito a yanzu haka Adamu yana kan gadon asibitin koyarwa na jami’ar Abuja yana samun kulawa, tuni shugaban karamar hukumar Gwagwalada Alhaji Kassim Mohammed ya kai masa ziyara don ganin halin da yake ciki.

Shi ma DPO na Yansandan Gwagwalada ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace yaron ya tsere, amma suna bin sawunsa domin samun nasarar kama shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel