Bashir Ahmad ya jinjinawa Ribadu bayan nasarar Buhari a kotun zabe

Bashir Ahmad ya jinjinawa Ribadu bayan nasarar Buhari a kotun zabe

A jiye Laraba, 11 ga Watan Satumba, 2019, kotun da ke sauraron korafin zaben shugaban kasa na bana ta yanke hukunci inda ta yi watsi da karar Atiku Abubakar, ta kuma tabbatar da nasarar APC.

Wani daga cikin Masu taimakawa shugaban kasa Muhammadu Buhari a wajen harkokin yada labarai, Bashir Ahmad, ya fito ya nuna farin cikinsa ga nasarar Mai gidan na sa a wannan karo.

Bashir Ahmad ya jinjinawa Malam Nuhu Ribadu na irin kokarin da ya yi a lokacin da ake wannan shari’ar na wata da watanni. Ahmad ya yabawa Ribadu ne a kan shafinsa na sadarwa na Tuwita.

Hadimin yake cewa: “Ina taya Congratulations to Mallam (Nuhu Ribadu) @NuhuRibadu murna game da nasarar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari @MBuhari ya samu yau a gaban kotu.”

Bashir ya cigaba da cewa: “Tun ranar farko da Mallam Nuhu (Ribadu) aka yi ta fama da kotun ta soma sauraron karar zaben. Kawo yanzu dai Ribadu bai ce komai ba game da hukuncin kotun.

KU KARANTA: Yadda zaman kotu ya nuna Atiku bai kaunar Talakawa – Hadimar Buhari

Tsohon shugaban hukumar EFCC, wanda ya nemi takarar gwamna da shugaban kasa a baya, shi ne ya rika tsayawa shugaba Buhari a kotu. Jiya an hange sa tare da su Alhaji Mamman Daura a zauren kotun.

Haka zalika Hadimin shugaban kasar ya bayyana cewa kotu ne karo na uku da Buhari ya doke Atiku. Na farko wajen zaben fitar da gwanin APC a 2014 a Legas, sai kuma babban zaben kasar da aka yi bana.

Atiku Abubakar ya zo na uku ne da kuri’u fiye da 900 a zaben tsaida ‘dan takarar shugaban kasa na APC na zaben 2015. Haka zalika a zaben 2019, da ya gwabza da Buhari, ya zo na biyu da ratar miliyan uku.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel