Lauretta Onochie ta caccaki Atiku bayan nasarar Shugaba Buhari

Lauretta Onochie ta caccaki Atiku bayan nasarar Shugaba Buhari

Bayan hukuncin da kotun da ke sauraron karar zaben shugaban kasa a zaben 2019 ta yi, Hadimar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Lauretta Onochie, ta fito ta yi magana bayan hukuncin.

Daya daga cikin Hadiman shugaban kasar ta ce tun farko sai da su ka gargadi Mabiyan Atiku Abubakar amma su ka yi kunnen kashi. A karshe dai kotun karar zabe ta yi fatali da karar PDP.

Misis Lauretta Onochie take cewa kallon yadda karar PDP ta sha kayi a gaban kuliya ya yi mata dadi inda ta kara da cewa Sai Baba Buhari. Onochie ta fito ta na wannan jawabi ne a shafin Tuwita.

Mai ba taimakawa shugaban kasar wajen yada labarai ya kafofin sadarwar yanar gizo ta nuna farin cikinta game da yadda aka yi watsi da karar PDP na cewa an aika sakamakon zabe ta na’ura.

KU KARANTA: Gwamnan hamayya ya taya Buhari murnar doke Atiku a kotu

Onochie ta ce sun fada cewa ba ayi amfani da uwar garke wajen aika sakamakon zabe a 2019 ba, haka zalika INEC ta fadi wannan amma duk ba a ji ba, kuma ba za a yarda ba, duk da hukuncin kotun.

Bayan nan kuma babbar Hadimar tace korafin da Atiku ya ke yi na cewa an saye kuri’ar masu zabe ta hanyar tsarin Trader Moni ya nuna cewa 'Dan takarar ya na yaki ne da shirin tallafawa marasa karfi.

Kotu ta yi watsi da karar da Atiku ya ke yi na cewa Farfesa Yemi Osinbajo ya yi amfani da Trader Moni wajen canzawa masu zabe ra’ayi inda ta ce shari'ar ta ba ta shafi mataimakin shugaban kasar ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel