Kotun zabe: Ban taba damun kai na tun farko ba – Inji Buhari

Kotun zabe: Ban taba damun kai na tun farko ba – Inji Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana nasarar da ya samu a gaban kotun da ke sauraron karar zaben shugaban kasa a 2019 a matsayin nasara ga ‘Yan Najeriyar da su ka zabe sa.

Muhammadu Buhari ya fito ya yi wannan jawabi ne jim kadan bayan kotu ta ba shi gaskiya a hukuncin da ta ayi Ranar Laraba, 11 ga Watan Satumba, 2019, inda aka yi watsi da karar 'dan takarar PDP.

Shugaban kasar ya nuna sam bai taba damuwa da karar da Abokan hamayya su ka shigar su na kalubalantar nasarar da ya samu a zaben na bana ba. Buhari ya ce yanzu gaskiya ta sake yin halin ta.

Shugaba Buhari ya yi wannan jawabi na farin ciki ne ta bakin Mai magana da yawunsa watau Femi Adesina. A jawabin da Adesina ya fitar, shugaban kasar ya ce yanzu kotu ta wanke sa a zaben.

KU KARANTA: Sanata Dino Melaye ya lallabi Mabiyansa da su kara hakuri

Buhari yake cewa ya sadaukar da wannan nasara da ya samu ga Ubangiji da kuma sauran ‘Yan Najeriya inda kuma ya yabawa Alkalai da su ka yi hukunci a kotu ba tare da tsoro ko son rai ba.

A wannan bayani da ya fito jiya daga fadara shugaban kasa, Adesina yake cewa shugaban kasar ya shirya aiki da kowa inda ya ce wadanda su ka sha kashin su na da damar zuwa gaban kuliya.

“Lokaci ya yi da za su ma sa kasa a gaban mu, mu yi aiki a matsayin daya, mu yi watsi da rikici da tirka-tirkar siyasar zaben da ‘yan Najeriya su ka fito su ka fito da karfinsu.” Inji shugaba Buhari.

‘Dan takarar PDP a zaben na 2019, Alhaji Atiku Abubakar ya shigar da kara kotu bayan zaben 2019 inda Lauyoyinsa su ka nemi ayi watsi da nasarar da Buhari ya samu. Atiku bai yi nasara ba.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Musulunci sai a bibiyi wannan shafi

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel