Tirkashi: Mintuna kadan ya rage a daura aure ango ya ce ya fasa auren gaba daya

Tirkashi: Mintuna kadan ya rage a daura aure ango ya ce ya fasa auren gaba daya

- Wani mutumi dan Najeriya ya dakatar da daurin aurensu a yayin da suke kan hanyar zuwa wajen daurin aure

- A wani bidiyo da yake yawo dai an hango angon yana amsa kiran waya, da ajiye wayar ya bayyana cewa ya fasa auren duka

- Bidiyon yanzu haka yana ta yawo a shafukan sada zumunta inda mutane ke ta faman maganganu a kan shi

Idan aka zo maganar abubuwan da zasu iya sanyawa a samu matsala a lokacin daurin aure, mutane da yawa suna kawo matsala irinta karancin abinci, saukar ruwan sama da dai sauransu. Mutane kadan ne suke tunanin cewa abokin aurensu zai iya sanyawa a dakatar da auren.

Wani bidiyo da yake ta yawo a shafukan sada zumunta ya bar mutane da yawa cikin rudani, bayan angon da aka bayyana sunanshi da Joe ya dakatar da daurin aurensu shida amaryarshi a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wajen daurin aurea Abuja.

A bidiyon an gano lokacin da angon ya tsayar da motar da suke ciki, inda ya kurawa wayarshi ta salula da amaryar tashi ido, kawai sai ji aka yi ya cewa amaryar ta shi ta fice mishi daga mota, inda ya nuna mata abinda ke cikin wayar.

KU KARANTA: Me suke nufi ne: Gwamnatin Afrika ta Kudu ta saka a kama 'yan Najeriya da suke kokarin dawowa gida saboda irin kisan gillar da ake musu a can

Amaryar tayi kokarin ta shawo kan angon wanda ya nuna bacin ranshi, inda har ta kai ga ta durkusa da guiwowinta tana rokar shi, sai dai kuma hakan bai yi aiki ba domin kuwa an jiyo muryarshi yana cewa ya fasa auren gaba daya ma.

A yadda bidiyon ya nuna, mutanen wajen kowa ya shiga rudani, inda abokanan shi suka yi kokarin shawo kanshi, haka kuma an hango dan uwan amaryar yana tunkarar angon akan abinda yasa ya batawa 'yar uwarshi rai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel