Me suke nufi ne: Gwamnatin Afrika ta Kudu ta saka a kama 'yan Najeriya da suke kokarin dawowa gida saboda irin kisan gillar da ake musu a can

Me suke nufi ne: Gwamnatin Afrika ta Kudu ta saka a kama 'yan Najeriya da suke kokarin dawowa gida saboda irin kisan gillar da ake musu a can

Wani rahoto da yake yawo ya nuna yadda gwamnatin kasar Afrika ta Kudu ta saka a dinga kama 'yan Najeriya wadanda suka shirya dawowa gida saboda irin kisan gillar da suke fuskanta daga 'yan kasar.

Wannan rahoto ya fito daga ofishin jakadancin Najeriya jiya Laraba 11 ga watan Satumba, rahoton ya bayyana cewa jami'an kasar ta Afrika ta Kudu suna zargin 'yan Najeriya da kokarin dawowa gida ba tare da cikakkun takardu ba.

Haka kuma rahoton ya nuna cewa jami'an kasar suna wahalar da ofishin jakadancin Najeriya na can, inda suke cewa 'yan Najeriyan da suke kokarin dawowa gida basu da cikakkun takardu, hakan yasa suke kama su suna kullewa, jaridar The Nation ta ruwaito.

Wani ma'aikacin ofishin jakadancin Najeriya ya bayyanawa manema labarai cewa: "Afrika ta Kudu na wahalar da 'yan Najeriya, jirgin da aka tura kasar ya isa tun karfe 4 na asuba, jami'an tsaron su suka fara bawa ma'aikatan mu matsala, suna cewa wai wasu 'yan Najeriya ba su da cikakkun takardu, hakan yasa suke kama su suna tambayarsu yadda aka yi suka shiga kasar Afrika ta Kudun.

KU KARANTA: Banci nanin ba nanin baza ta cini ba: Babu wanda na yiwa alkawarin motoci 10 idan Buhari yayi nasara - Dino Melaye

"Jirgin yana kasa tun karfe 4 na asuba, basa jin dadi yadda Najeriya za ta kwashe mutanenta, basa son duniya ta san cewa Najeriya na kwashe mutanenta."

Jiya dai muka ruwaito muku cewa 'yan Najeriya sun kammala shiri tsaf domin dawowa gida Najeriya, bayan irin halin da suke ciki na kisan gillar da ake yi musu a kasar Afrika ta Kudu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel