Kar ku damu ko kadan saboda har yanzu mune da nasara - Dino Melaye na rarrashin mabiyansa

Kar ku damu ko kadan saboda har yanzu mune da nasara - Dino Melaye na rarrashin mabiyansa

- Duk da irin tashin hankalin da Sanata Dino Melaye yake ciki na dakatar da shi da aka yi a matsayin Sanatan jihar Kogi ta Yamma

- Da kuma faduwa da yayi zaben fidda gwani na gwamnan jihar Kogi a jam'iyyar PDP, hakan bai saka Sanatan ya saduda ba

- Sanatan ya wallafa wani hoto a shafinsa na Instagram, inda yake bayyana cewa kada kowa ya damu saboda har yanzu sune da nasara

Alamu sun nuna cewa Sanata Dino Melaye yana cikin tsananin tashin hankali saboda abubuwa guda biyu da suka faru da shi. Abu na farko shine, kotu ta tsige shi daga kan kujerar shi ta Sanata, inda ta bukaci a sake sabon zaben Sanata a yankin jihar Kogi ta Yamma inda yake wakilta a majalisar tarayya.

Abu na biyu shine, ya sha kasa a zaben fidda gwani da aka yi na babbar jam'iyyar adawa ta People Democratic Party PDP a jihar ta Kogi.

Duk da wannan abubuwa da suka faru da Sanatan bai sa ya saduda ba, inda ya shiga shafinsa na Instagram ya wallafa wani hoto a lokacin da ya karbi wasu baki a ofishin sa, inda a kasan hoton yayi rubutu kamar haka: "Kar ku damu, zamu samu nasara."

KU KARANTA: Tirkashi: Mintuna kadan ya rage a daura aure ango ya ce ya fasa auren gaba daya

Wannan rubutu da Sanatan yayi ya jawo kace nace a shafin na shi na Instagram, inda wasu mutane suka mayar da abin kamar barkwanci suka dinga tsokanar Sanatan kowa da irin abinda yake fada dangane dashi, ma'ana kowa na fadar albarkacin bakinsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel