Hukuncin kotun zabe: Wani dan majalisa ya koka bayan yan bindiga sun kai mamaya gidajen sa

Hukuncin kotun zabe: Wani dan majalisa ya koka bayan yan bindiga sun kai mamaya gidajen sa

Wani dan majalisar wakilai mai wakiltan mazabar Abi/Yakurr majalisar dokokin kasar, Dr Alex Egbona, a jiya Talata, 10 ga watan Satumba, ya koka cewa an kai wa gidajensa da ke kauye da Calabar mummunan hari, yan kwanaki bayan ya yanke shawarar kalubalatar hukuncin kotun zabe akan zabensa a kotun daukaka kara.

Harin farko da yan bindiga suka kai ya kasance a gidansa da ke Ekureku kimanin sa’o’i 24 bayan hukuncin kotun zaben wacce ta bai wad an takarar PDP, John Gaul Lebo nasara.

Da yake Magana da manema labarai bayan harin, Egbona yace: “A jiya kuma, na samu sako cewa wasu yan bindiga sun kai hari kauyena da misalin tsakar dare sannan suna ta harbi ba kakkautawa. A daidai wannan lokacin kuma wasu rukunin yan bindiga suka je gidana a Calabar suna ta harbe-harbe kafin suka bar wajen.

“Na rasa gane dalilin kai hari gidajena. Idan kotun zabe ta yake hukuncin cewa dan takarar PDP yayi nasara a kotun zaben, ina da ikon daukaka kara sannan a bar ni a raye na bibiyi shari’ana a kotun daukaka kara.

“Wannan barazanar ba zai kaimu ko ina ba. Zan je kotun daukaka kara domin gwada doka sannan babu wani barazana da zai hana ni. Kudirina na daukaka kara shine son tabbatar da cewa mutane ne suka zabe ni sannan cewa ba za a kwace wannan nasarar ta hukuncin bayan gida ba.

KU KARANTA KUMA: Rochas Okorocha ya taya shugaba Buhari murnar nasara a kotun zabe

“Ina roki jami’an doka a jiharmu da su tabbatar da tsarina. Na ja hankalin yan sanda a karamar hukuma na akan barazana ga tsaro na sannan na yarda cewar za su dauki mataki.”

Dan majalisar ya kuma yi zargin cewa ya amsa kiran waya inda ake masa barazana da gargadin cewa kada ya daukaka kara “ idan ina so na ci gaba da rayuwa.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel