Yadda aka tarbi gawar marigayi Mugabe a Zimbabwe cikin alhini

Yadda aka tarbi gawar marigayi Mugabe a Zimbabwe cikin alhini

A ranar Laraba, 11 ga watan Satumba, gawar marigayi tsohon shugaban kasar Zimbabwe, Robert Mugabe, ta iso kasar bayan mutuwarsa a kasar Singapore.

Mugabe, tsohon dan gwagwarmaya, ya mutu ne ranar Juma'a yana da shekaru 95 a duniya.

Lafiyar tsohon shugaban kasar ta kara tabarbarewa ne bayan wani babban jami'in soja mai kusanci da shi ya jagoranci yi masa juyin mulki a shekarar 2017.

Ya mutu ne a Singapore, kasar da ya saba zuwa domin duba lafiyarsa. Gwamnatin kasar Zimbabwe ta aika wakilai karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Kembo Mohadi, zuwa kasar Singapore domin dauko gawar marigayi Mugabe zuwa gida.

Da safiyar ranar Laraba ne aka dauko gawar Mugabe inda aka rako ta zuwa filin jirgin sama bisa rakiyar jami'an tsaro.

DUBA WANNAN: Dalibar makarantar firamare ta kashe kan ta bayan jinin al'ada ya bata mata kayan makaranta saboda rashin 'kunzugu'

Ana sa ran shugaban kasar China, Xi Jinpin, tsohon shugaban kasar Cuba, Raul Castro, da dumbin sauran shugabannin kasashen Afrika zasu halarci jana'izar Mugabe, kamar yadda fadar shugaban kasar Zimbabwe ta bayyana.

Marigayi Mugabe ya kasance daya daga cikin shugabannin kasashen Afrika da sunansu ya yi fice.

Ana yawan alakanta Mugabe da karin magana na barkwanci masu cike da hikima da basira.

Yadda aka tarbi gawar marigayi Mugabe a Zimbabwe cikin alhini

Yadda aka tarbi gawar marigayi Mugabe a Zimbabwe cikin alhini
Source: Twitter

Yadda aka tarbi gawar marigayi Mugabe a Zimbabwe cikin alhini

Alhinin mutuwar marigayi Mugabe a Zimbabwe
Source: Twitter

Yadda aka tarbi gawar marigayi Mugabe a Zimbabwe cikin alhini

Isowa gawar marigayi Mugabe Zimbabwe
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel