Nasarar Buhari a kotu: Wike ya taya Shugaban kasan murna a kan nasarar da ya samu a kotun zabe

Nasarar Buhari a kotu: Wike ya taya Shugaban kasan murna a kan nasarar da ya samu a kotun zabe

Gwamnan Jihar Rivers, Nyesom Wike wanda ya ci zabe a karkashin jam’iyyar PDP ya taya Shugaba Muhammadu Buhari murna a bisa nasarar da ya samu a kotun zabe ranar Laraba 11 ga watan Satumba, 2019.

A wani zance na Gwamnan da ya fitar ranar Laraba ya roki Shugaban kasa cewa yayi amfani da wannan nasara domin kawowa kasarsa cigaba.

KU KARANTA:Shari’ar Buhari da Atiku: PDP za ta garzaya Kotun Koli, ta ce akwai rashin gaskiya cikin wannan hukunci

Ya kuma sake yin kira ga Shugaba Buhari kan ya jajirce wurin yin ayyukan da za su hada kan al’ummar kasa baki daya domin gujewa rabuwar kawuna.

A ranar Laraba 11 ga Satumba ne kotun dake sauraron korafi a kan zaben Shugaban kasa ta yi watsi da karar PDP da dan takararta Atiku Abubakar wanda yake kalubalantar nasarar Shugaba Buhari da APC a zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu.

A wani labarin kwatankwacin wannan kuwa, zaku ji cewa jam’iyyar PDP za ta garzaya zuwa kotun koli domin sam ba ta aminta da wannan hukunci na kotun zabe ba.

Mai magana da yawun jam’iyyar Mista Kola ne ya fitar da wannan bayanin inda ya ce babu komi cikin hukuncin nan na kotun zabe in banda rashin gaskiya a bayyane.

Ya kuma roki al’ummar Najeriya musamman magoya bayan jam’iyyarsu ta PDP da su kwantar da hankalinsu shari’a yanzu aka fara saboda za su kai kara kotun koli.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel