Rochas Okorocha ya taya shugaba Buhari murnar nasara a kotun zabe

Rochas Okorocha ya taya shugaba Buhari murnar nasara a kotun zabe

Tsohon gwamnan jihar Imo kuma sanata mai wakiltan Yankin Imo ta Kudu, Rochas Okorocha ya bayyana hukuncin kotun zabe da ta tabbatar da zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari a matsayin nasara ga masoyan damokradiyya.

Okorocha wanda ya taya Shugaban kasar murna a wani jawabi dauke da sa hannun hadiminsa, Mista Sam Onwuemeodo, ya bayyana cewa nasarar zai sa shugaban kasar ya kara kokari.

Yace hakan zai bashi damar kara kaimi wajen ganin ci gaban kasar da zaman lafiya da hadin kanta.

Tsohon gwamnan ya yaba ma mambobin kotun zaben kan “yin aiki nagari wanda zai sanya kasar yin alfahari”.

Ya kuma yaba ma Atiku Abubakar, dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kan “gudunmawarsa ga damokradiyyar kasar”.

Okorocha ya kuma bayyana da dukkanin wannan, akwai haske a lamarin damokradiyyar kasar.

A wani lamari makamancin haka Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murna kan nasarar da yayi a kotun zaben shugaban kasa, a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba.

KU KARANTA KUMA: Buhari ya yi magana a karon farko game da nasarar daya samu a kan Atiku Abubakar

Gwamnan ya jinjinawa hukuncin kotun zaben shigaban kasar da ta tabbatar nasarar Buhari a zaben 2019 a matsayin tsantsar adalci ga shari’an.

Ya kuma yiwa shugaban kasar fatan samun tarin nasara a mulkinsa na biyu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel