FG ta amince da kara kaso 2.2% a kan kudin harajin kayan amfani

FG ta amince da kara kaso 2.2% a kan kudin harajin kayan amfani

Majalisar zartar wa ta tarayya (FEC) ta amince da kara kudin harajin kayan amfani (VAT) daga 5% zuwa 7.2%.

Ministar kudi da tsare-tsare, Zainab Ahmed, ce ta sanar da hakan ga manema labarai a karshen zaman majalisar na ranar Laraba.

Sai dai, karin ba zai tabbata ba sai majalisa ta yi kwaskwarima ga dokar kara kudin haraji a kan kayan amfani wacce aka kirkira a shekarar 1994.

A shekarar 1994 ne tohon shugaban kasa a mulkin soji, Sani Abacha, ya gabatar da tsarin VAT kuma ya kai shi zuwa kaso 5%.

DUBA WANNAN: Nasarar Buhari a Kotu: Gwamna Bello ya yi watsi da kudi, jama'a sun daka 'wawaso'

Tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya kara shi zuwa kaso 10% a karshen wa'adinsa na biyu da ya kare a shekarar 2007. Sai dai, tsohon shugaban kasa, marigayi Umar Musa Yar'adu, ya soke karin bayan kungiyar kwadago ta nuna adawarta a kan karin da Obasanjo ya yi.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ne ya jagoranci zaman FEC na ranar Laraba, wanda suka shafe tsawon sa'o'i 7 suna tattauna wa.

Ministar ta ce FEC ta bayar da umarni fara tuntubar gwamnotocin jihohi da kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki kafin sabon tsarin ya fara aiki a cikin shekarar 2020.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel