Adamu Adamu ya bayyana Buhari ya kashe N1,400,000,000 wajen manyan ayyuka

Adamu Adamu ya bayyana Buhari ya kashe N1,400,000,000 wajen manyan ayyuka

Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kashe makudan kudade wajen samar ma yan Najeriya manyan ayyukan more rayuwa, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Adamu ya bayyana haka ne yayin wani taron kungiyar magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Muhammadu Buhari Enduring Legacy Network (MBEL-N) daya gudana a garin Abuja, inda yace Buhari ya kashe kimanin naira tiriliyan 1.4 a manyan ayyuka.

KU KARANTA: Buhari ya yi magana a karon farko game da nasarar daya samu a kan Atiku Abubakar

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Adamu, wanda ya samu wakilcin mataimakin darakta a ma’aikatar ilimi, Ben Gong, yace wadannan kudade basu cikin lissafin kudaden da gwamnatin ta kashe wajen biyan albashin ma’aikata da kudaden fansho.

Sa’annan ya baiwa mahalarta taron tabbacin gwamnatin Buhari za ta tabbatar da cika dukkanin alkawurran da ta daukan ma yan Najeriya, kuma za ta dage wajen ciyar da bangaren ilimi gaba.

Wasu daga cikin ayyukan da gwamnatin za ta mayar da hankali a bangaren ilimi sun hada da rage yawan daliban dake gararamba a kan tituna tare da sanyasu a makaranta, da kuma tabbatar da kyakkyawar alaka tsakanin gwamnati da kungiyoyin ma’aikata dake bangaren ilimi.

A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana nasarar daya samu a gaban kotun sauraron koke koken zaben shugaban kasa na 2019 inda dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kai shi kara, a matsayin nasara ga jama’an Najeriya.

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa, Femi Adesina, inda yace wannan nasara, nasara ce ga dimbin jama’an da suka zabeshi a a karo na biyu a ranar 23 ga watan Feburairun shekarar 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel