Nasarar Buhari a Kotu: Gwamna Bello ya yi watsi da kudi, jama'a sun daka 'wawaso'

Nasarar Buhari a Kotu: Gwamna Bello ya yi watsi da kudi, jama'a sun daka 'wawaso'

An samu cunkuson ababen hawa a daidai unguwar da ke kan babban titin Abuja zuwa jihar Kogi da yammacin ranar Laraba sakamakon daka wawaso da jama'a suka yi a kan takardun kudin da gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya watsa yayin da yake wuce wa.

Bello, wanda ke kan hayarsa ta zuwa Lokoja daga birnin tarayya, Abuja, ya sa an rage saurin tafiyar motocin tawagarsa a daidai kwanar 'Madam Mercy' tare da fito da bandir uku na takardun N500, wadanda ya watso wa jama'a dake wuce wa.

Wakilin jaridar Daily Trust da lamarin ya faru a kan idonsa ya ce gwamnan ya sauke gilashin motar da yake ciki tare da yin alamar 4+4 da yatsun hannunsa yayin da wasu zauna gari banza a tashar motoci ta 'Wazobia' ke yi masa ihun jinjina tare da ruga wa da gudu domin su kwashi kudin da ya watso.

DUBA WANNAN: Daliba ta kashe kan ta bayan jinin al'ada ya bata mata kayan makaranta saboda rashin 'kunzugu'

Jaridar Daily Trust ta ce cunkuson ababen hawan ya tarwatse cikin lokacin da bai wuce dakika goma ba.

Rahoton jaridar ya bayyana cewa wasu jama'a da ke wuce wa, masu kananun sana'o'i a gefen hanya da 'yan acaba sun bar harkokinsu tare da ruga wa da gudu domin su kwashi rabonsu daga cikin kudaden da gwamna Bello ya watso kan titi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel