Gwamna Bello ya taya Buhari murnar samun nasara a kotun zabe

Gwamna Bello ya taya Buhari murnar samun nasara a kotun zabe

Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya taya Shugaban kasa Muhammadu Buhari murna kan nasarar da yayi a kotun zaben shugaban kasa, a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba.

Gwamnan ya jinjinawa hukuncin kotun zaben shigaban kasar da ta tabbatar nasarar Buhari a zaben 2019 a matsayin tsantsar adalci ga shari’an.

Ya kuma yiwa shugaban kasar fatan samun tarin nasara a mulkinsa na biyu.

Bello a Wani jawabi daga babban sakataren labaransa, Muhammed Onogwu yace hukuncin kotun zaben wanda ya kori karar da Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Atiku Abubakar suka shigar akan Buhari, da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki ya nuna cewa “bangaren shari’a bata damu da kanzon kurege da kullin da wasu makirai suka yi ba."

Daga nan Bello ya bukaci PDP da Atiku da su amince da hukuncin sannan su hada hannu da Shugaban kasar wajen kai kasar matakin ci gaba.

Ya kuma bukaci shugaban kasa Buhari da tawagarsa da su jajirce wajen isar da manufofin Next Level.

KU KARANTA KUMA: Kotun zaben Shugaban kasa: Muhimman hukunce-hukunce 7 da aka yanke zuwa yanzu

A halin da ake ciki mun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana nasarar da ya samu a gaban kotun sauraron koke koken zaben shugaban kasa na 2019 inda dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kai shi kara, a matsayin nasara ga jama’an Najeriya.

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa, Femi Adesina, inda yace wannan nasara, nasara ce ga dimbin jama’an da suka zabe shi a karo na biyu a ranar 23 ga watan Feburairun shekarar 2019, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel