Buhari ya yi magana a karon farko game da nasarar daya samu a kan Atiku Abubakar

Buhari ya yi magana a karon farko game da nasarar daya samu a kan Atiku Abubakar

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana nasarar daya samu a gaban kotun sauraron koke koken zaben shugaban kasa na 2019 inda dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kai shi kara, a matsayin nasara ga jama’an Najeriya.

Buhari ya bayyana haka ne ta bakin kaakakinsa, Femi Adesina, inda yace wannan nasara, nasara ce ga dimbin jama’an da suka zabeshi a a karo na biyu a ranar 23 ga watan Feburairun shekarar 2019, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Da dumi dumi: Jirgin farko na yan Najeriya ya dawo gida daga kasar Afirka ta kudu

“Mai gaskiya baya tsoron komai, ban taba damuwa ba ko kadan saboda na san yan Najeriya da kansu suka zabeni, kuma a yanzu gaskiya ta yi halinta.” Inji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Buhari ya kara da cewa ya sadaukar da nasarar daya samu ga Allah Ubangiji, sa’annan ga kafatanin yan Najeriya, bugu da kari ya jinjina ma bangaren sharia da ta gudanar da aikinta ba tare da tsoro ko son kai ba.

Haka zalika Buhari ya mika hannun abota ga wadanda suka kai shi kara sakamakon rashin gamsuwa da sakamakon zaben, inda yace suna da yancin yin hakan a tsarin dimukradiyya.

Daga karshe yace: “Tunda dai a yanzu kotu ta yanke hukunci, lokaci yayi da kasar Najeriya za ta cigaba a matsayin tsintsiya madaurinki daya, ba tare da tuna baya da duk wasu abubuwa da ka iya kawo cikas ga cigaban kasar.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel