Tirkashi: Zaku zageni ku ci banza, amma baza ku taba Kaduna ku kwana lafiya ba - El-Rufai yayi gargadi

Tirkashi: Zaku zageni ku ci banza, amma baza ku taba Kaduna ku kwana lafiya ba - El-Rufai yayi gargadi

- Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa kowanne mutum zai iya zagin shi ya ci banza ya kwana lafiya

- Amma kuma duk wanda ya yada wani labari da zai kawo rashin kwanciyar hankali a fadin jihar Kaduna to tabbas zai dandana kudarsa

- Gwamnan ya bayyana hakanne a wani martani da yake mayarwa wani mutumi da ya kira shi da makaryaci a shafin sada zumunta na Twitter

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, ya sake yin wani sabon gargadi akan mutanen da suke wallafa labarai na karya akan jihar Kaduna.

Idan ba a manta ba, a wajen gabatar da wani littafi jiya a Kaduna, gwamnan ya gargadi mutanen da suke wallafa labaran karya akan jihar Kaduna a shafin Twitter, inda ya bayyana musu cewa suyi a hankali akan abubuwan da suke rubuta domin kuwa yana kallon duka abubuwan da suke wakana, kuma zai dauki mataki kwakkwara akan wanda suka rubuta labarin kanzon kurege.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Inda za a koma cin naman mutum da za a samu sauyin yanayi a duniya - Wani masani ya bayar da dalilin shi

Wani matashi mai amfani da shafin sadarwa na Twitter mai suna Chuks Akunna ya kira gwamnan da makaryaci akan ya bayyana cewa ya samarwa da matasa aikin yi guda dubu hamsin.

Da yake mayar da martani akan maganar mutumin, gwamnan ya bayyana cewa kiranshi da makaryaci ba komai bane, amma kuma tayar da zaune tsaye a jihar Kaduna a shafukan sadarwa dole zai dauki mataki a kai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel