Tashin hankali: Mai gadi ya kashe ubangidansa ya jefa gawar a cikin tankin ruwa

Tashin hankali: Mai gadi ya kashe ubangidansa ya jefa gawar a cikin tankin ruwa

- Wani mutumi dan kasar Labanon ya gamu da ajalinsa a yayin da aka tsinci gawarsa a cikin tankin ruwa a gidansa

- Sai dai ana zargin mai gadinsa mai suna Adamu Mohammed da aikata wannan aika-aika bayan an gano cewa sun samu hatsaniya kwana daya da samun gawar mutumin

- An bayyana cewa mutumin ya dauki Adamu aiki ne na gadi sai kuma ya tarar cewa yana yi masa 'yan dauke-dauke, hakan yasa yayi masa magana, amma washe gari sai gawar shi aka gani a cikin tankin ruwa

An samu gawar wani mutumi dan kasar Labanon mai suna Basan Khodari a cikin tankin ruwa a gidansa dake birnin Legas ranar Talatar nan da ta gabata a da yamma.

Ana zargin wani mai gadinshi wanda marigayin ya dauka aiki mai suna Adamu Mohammed, bayan an nemi wasu abubuwa a gidan nashi da suka hada da AC, talabijin injin janareto an rasa bayan samun gawar mutumin.

Khodari dai ya dawo daga tafiyar da yayi zuwa birnin Abuja sai ya tarar da mai gadin nasa Mohammed da wasu abokanan shi sun sace mishi wasu abubuwa a gidan shi a ranar 9 ga wannan watan. Sai yaje ya samu mai gadin akan dalilin da yasa ya kawo masa baki gida, an bayyana cewa wannan magana da mai gidan ya yiwa mai gadin ita ce ta saka mai gadin jin haushi.

KU KARANTA: Ina jira naga dan iskan da zai zo yace mini nayi rijista kafin na cigaba da fim - Sakon Baban Chinedu ga Afakallahu

Wasu wanda aka yi cacar bakin tsakanin Mohammed da mai gidansa a gabansu sun bayyana cewa sun yi mamaki da suka ga gawar mai gidan a cikin tanki da misalin karfe 2 na rana.

Jaridar The Nation ta bayyana cewa hannayen mutumin da kafafun duk an daure su kafin a tsunduma shi a cikin tankin ruwan, sannan kuma an ga wani rauni a jikin marigayin.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Bala Elkana ya tabbatar da faruwar lamarin sannan ya bayyana cewa yanzu haka an kama wasu da ake zargin su da wannan laifin. Haka kuma ya kara da cewa jami'ansu sun gano wata bindiga da harsashi a dakin mai gadin a lokacin da suke bincike.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel