Mutumin da ya kashe shanu 4 ya gurfana gaban kotu

Mutumin da ya kashe shanu 4 ya gurfana gaban kotu

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta shigar da karar Samson Aku, manomi mai shekaru 67 bisa laifin kashe dabbobi guda hudu.

Manomin wanda ke zaune a unguwar Bwari dake Abuja ana zarginsa ne da laifin kisan dabbobin Idris Wada wanda yake makiyayi ne.

KU KARANTA:NDLEA ta tarwatsa wata katafariyar gonar wiwi a jihar Edo

Wada a lokacin da yake bayyana jawabinsa ga kotu ya ce a ranar Laraba ya rasa shanunsa guda hudu a lokacin da Aku ya farma dabbobin nasa.

Lauyan Idris Wada ya shaidawa kotun cewa, Aku yayi amfani ne da adda inda yayi ta sarar shanun har sai da suka sheka lahira.

A cewar Wada, ya sayar da shanunsa guda biyu N70,000 wadanda ba su riga sun mutu ba. Sannan kuma ko wace daya da aka kashe tana zaman N180,000 ne.

“Yaro na ne ya kirani a wayar salula cewa in yi gaggawar zuwa gona saboda an farma shanuna guda shida. Yaron nawa yana da gonarsa ne a kusa da tawa.

“Ko da na iso gonar guda hudu sun riga sun mutu, inda kuma na samu biyu na kokarin mutuwa sai na yanka su gabanin su karasa na kira wani mai sayar da nama ya saye su.” Inji Wada.

Lauyan wanda ake tuhuma, Abubakar Suleiman ya ce sam wanda ake zargin bai aikata wannan laifin ba, inda ya ce ai mai shanun tare da yaronsa ne suka yanka dabbobin da kansu.

Ya kara da cewa, makiyayin ba shi da wata hujja ta cewa kashe masa dabbobinsa a kayi saboda kiransa aka yi a waya ya zo ba wai a gabansa abin ya faru ba.

Bayan da alkalin kotun ya kammala sauraron ta bakin bangarorin biyu, ya daga karar zuwa ranar Litinin mai zuwa inda za a cigaba da zama.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel