Yanzu-yanzu: An tashi, Buhari ya lallasa Atiku a kotu

Yanzu-yanzu: An tashi, Buhari ya lallasa Atiku a kotu

Bayan kwashe akalla sa'o'i takwas ana zaman kotu kan shari'ar dake tsakanin shugaba Muhammadu Buhari na APC da Atiku Abubakar na PDP, shugaban kwamitin Alkalan kotun, Mohammed Garba, ya yi watsi da karar da PDP da Atiku suka shigar.

Alkaln ya bayyana hakan ne bayan yanke hukunci daya bayan daya kan zarge-zargen da Atiku da PDP sukayi kan nasarar shugaba Muhammadu Buhari na cewa:

1. Bai cancanci takarar zabe ba saboda bai da takardan shaidan halartan makarantan sakandare

2. An yi amfani da Sojoji da yan sanda wajen magudi zaben

3. Kuri'un da hukumar INEC ta sanar ba kai yawan wanda ke shafin yanar gizonsu

4. An ci mutuncin yan jam'iyyar PDP a jihohi 11 lokacin zabe, da sauransu

5. Mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinajo, ya yi amfani da shirin Tradermoni wajen sayen kuri'u

KU KARANTA: Da duminsa: Atiku dan Najeriya ne, kotun zabe ta yanke hukunci

Bayan sauraron dukkan hujjojin bangarorin guda biyu, kwamitin alkalan na mutane biyar sun yi ittifakin cewa a yi watsi da karar PDP da Atiku.

Saboda haka, kotun ta tabbatar da cewa shugaba Muhammadu Buhari ne ya lashe zaben 23 ga watan Febrairu, 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Tags:
Mailfire view pixel