NDLEA ta tarwatsa wata katafariyar gonar wiwi a jihar Edo

NDLEA ta tarwatsa wata katafariyar gonar wiwi a jihar Edo

Hukumar hana sha da kuma fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya wato NDLEA reshen jihar Edo ta ce ta gano tare da tarwatsa wata katafariyar gonar wiwi mai fadin eka biyu a jihar.

Kwamandan hukumar na jihar, Mista Buba Wakawa ne ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Najeriya, NAN wannan labarin a Benin ranar Laraba 11 ga watan Satumba.

KU KARANTA:Ganduje ya ba matasa 60 tallafin naira miliyan 30 domin gudanar da sana’a

Wakawa ya ce gonaki guda biyu inda suke a karamar hukumar Ovia ta arewa da kuma Etsako ta yamma. An samu kimanin kilo 248,088 na danyen ganyen tabar wiwin a gonakin.

Ya kara da cewa, hukumar NDLEA ta karbe kilo 452.36 na ganyen wiwi, kwayar Tramadol da kuma Diazepam.

A cewarsa an samu wadannan nasarorin ne a cikin watan da ya gabata. Kuma an samu nasarar damke mutane 11 wadannan suke fataucin miyagun kwayoyi a jihar, biyar maza yayin da sauran shida kuwa mata ne.

Mutanen da aka kama duk sun amsa laifin da ake tuhumarsu da shi inda suka amsa cewa lallai sun kasance su masu fataucin miyagun kwayoyi ne.

Kwamandan ya nuna damuwarsa a dalilin irin gurbacewar tarbiya da wannan mummunan aiki na fatauci miyagun kwayoyi yake kawowa a cikin al’umma, inda ya ce: “Matasa da dama sun zama mashaya a yau, a sakamakon haka suke bijirewa iyayensu a gida babu kuma batun zuwa makaranta sai dai yawon gantali na banza.

“Daga nan ne wasunsu ke kama hanyar sata, fashi da makami, shiga kungiyoyin asiri da kuma sauran nau’ukan miyagun ayyuka dake addabar al’umma a yau.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Online view pixel