Wani mutum da ya yi sojan gona a matsayin CP ya damfari sanatan arewa N1.8m

Wani mutum da ya yi sojan gona a matsayin CP ya damfari sanatan arewa N1.8m

'Yan sanda a Zamfara sun kama wani mutum mai suna Ibrahim Mohammed Maigandi da ya yi wa kwamishinan 'Yan sanda Usman Nagogo sojan gona ya damfari sanata mai wakiltan Zamfara ta Yamma, Lawal Hassan Dan Iya naira miliyan 1.8.

A yayin da ake holen wanda ake zargin a hedkwatan rundunar, SP Muhammed Shehu ya ce wanda ake zargin dan asalin garin Moriki ne a karamar hukumar Zurmi. Ya ce an kama shi ne bayan sanatan ya shigar da rahoto cewa wani da ya yi ikirarin shine CP Usman Nagogo ya kira shi ya nemi ya bashi goron sallah.

Ya ce bayan wanda ake zargin ya kira waya, Sanata Dan Iya ya umurci hadiminsa ya karbi lambar asusun ajiyar bankinsa ya tura masa N200,000 kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

DUBA WANNAN: An kama 'yan kungiyar Oro guda tara da suka kai wa musulmi hari a Ogun

"Daga bisani, wanda ake zargin ya sake kiran sanatan ya shaida masa cewa ya bashi guraben daukan aikin 'Yan sanda shida amma ya nemi ya biya shi naira miliyan 2. Sanatan ya kuma sake fadawa hadiminsa ya tura naira miliyan 1.6 a asusun wanda ake zargin," a cewar Shehu.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce daga baya an binciko wanda ake zargin a Gusau inda aka kama shi da mota kirar Marsandi da kudi naira miliyan 1.4 kuma an fara bincike domin gano sauran 'yan kungiyar damfarar ta su.

A halin yanzu, wanda ake zargin ya amsa laifinsa inda ya ce ya san abinda ya aikata ba shi da amfani. Ya ce ya kammala karatu a Polyteknik kuma yana da matan aure biyu da 'ya'ya takwas.

"Na aikata laifin ne domin in samu kudin asibiti na mata ta da ke fama da cutar daji."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel