Yanzu-yanzu: Mutum biyu sun mutu, an nemi da dama an rasa sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai kauyen Yongogba

Yanzu-yanzu: Mutum biyu sun mutu, an nemi da dama an rasa sakamakon harin da 'yan bindiga suka kai kauyen Yongogba

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan daban Jukun ne sun kai farmakia safiyar ranar Laraba inda suka kashe mutane biyu a kauyen Yongogba da ke karamar hukumar Takum na jihar Taraba.

Wani mazaunin kauyen mai suna Kester Iorhemba ya shaidawa The Punch cewa maharan da suka shiga kauyen daga Takum sun kone dukkan gidajen da ke garin tare sace musu kayyaki.

A cewar Iorhemba, maharan sun shigo kauyen kan babura da kuma motoci kirar Toyota Hilux biyu misalin karfe 8.45 na safiyar yau inda suka kashe mutane biyu kuma an nemi wasu an rasa.

Ya yi bayyanin cewa maharan sun shigo kauyen ne ta cikin gonar TY Danjuma inda suka fara kashe mutane biyu da ke gonakinsu sannan suka karaso cikin garin suka kone dukkan gidajen.

DUBA WANNAN: An kama 'yan kungiyar Oro guda tara da suka kai wa musulmi hari a Ogun

Wani da ya ganewa idonsa abinda ya faru ya ce akwai yiwuwar wanda suka mutu sun fi buyu duba da cewa akwai mutane da yawa kan hanyar gona. Ya yi kira da gwamnan jihar Darius Ishaku ya dauki matakin gaggawa na kawo karshen kashe-kashen.

Ya ce, "Ina hanyar zuwa gona na hango motocci Toyota Hilux biyu da babura suna zuwa kauyenmu.

"Ban iya sanar da 'yan uwan na da ke gida ba a wayan tarho saboda rashin kyawun sabis.

"Har yanzu ba a gano wasu mutane ba kuma ina kyautata zaton maharan sun kashe ne shi yasa ba a gansu ba har yanzu.

"Gwamnan mu da ya ki amince a kafa kwamitin bincike kan kashe-kashen ya ce zai iya kawo karshen rikicin saboda haka ina rokon sa ya dauki mataki cikin gaggawa."

Duk yunkurin da aka yi na ji ta bakin mai magana da yawun 'yan sandan jihar, ASP David Misal ya ci tura domin bai amsa wayarsa ba kuma bai amsa sakon tes ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel