Da dumi-dumi: Babu hujjar cewa INEC ta tura sakamakon zabe zuwa wata na’ura, kotu ta yanke hukunci

Da dumi-dumi: Babu hujjar cewa INEC ta tura sakamakon zabe zuwa wata na’ura, kotu ta yanke hukunci

Kotun da ke sauraron korafe-korafen zaben Shugaban kasa ta kaddamar da cewar babu wani hujja dake nuna cewa hukumar zabe mai zaman kanta (INEC), ta tura sakamakon zaben Shugaban kasa da aka yi watannin baya zuwa wata na’ura.

Kotun, da take yanke hukunci akan karar da Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP, ta bayyana cewa masu karar sun gaza tabbatar da wanzuwar wata na’urar INEC ko kuma cewar hukumar zabe ta tura sakamako ta na’ura.

Kotun ta yanke hukunci cewa babu wata doka a Najeriya da ta yarda da tura sakamakon zabe ta na’ura ko kuma tura sakamakon ta hanyar amfani da ‘card reader’ wato na’utrar tantance katunan zabe.

KU KARANTA KUMA: Kotun zaben Shugaban kasa: Muhimman hukunce-hukunce 7 da aka yanke zuwa yanzu

"Nayi nazari sosai sannan na tantance takardu 28 na zaben INEC wanda masu karr suka gabatar, ban ga inda aka ce akwa na'urar tura sakamakon zabe ba," inji jagoran kotun zaben, Justis Mohammed Garba.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kotun zaben shugaban kasa ta yi watsi da zargin cewa dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ba haifaffan dan Najeriya bane kuma bai cancanci takaran zabe.

Wannan hukunci ya biyo bayan ikirarin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da shugaba Muhammadu Buhari cewa Atiku ba haifaffen dan Najeriya bane saboda a lokacin da aka haifesa, garin Jada ba ta cikin Najeriya, tana Kamaru.

A hukunci na shida da kotu ta yanke, ta ce ba tada hurumin tabbatar da ko rashin tabbatar da cewa dan takara bai cancanta ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel