Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a matatar man fetur ta kasa, NNPC da ke Ibadan

Yanzu-yanzu: Gobara ta tashi a matatar man fetur ta kasa, NNPC da ke Ibadan

- Gobara ta tashi a matatar man fetur ta kasa a reshen ta da ke Apata, Ibadan

- Gobarar ta fara ne a sashin lodin mai na matatar

- Shekaru biyu kenan da aka kara bude matatar bayan da tayi shekaru ba ta aiki

A ranar Laraba ne gobara ta tashi a ma'ajiyar man fetur ta kasa da ke Apata, Ibadan.

Gobarar ta fara ne daga sashin lodi kamar yadda ma'aikaci a hukumar ga sanarwa wakilin jaridar Punch.

Gobarar ta kawo matsalar cunkushewar titin Apata zuwa Abeokuta.

A halin yanzu dai babu bayani gamsasshe daga hukumar matatar domin 'yan kwana-kwana na ta kokarin kashe wutar.

KU KARANTA: Kotun zabe: Gwamna Dapo Abiodun da Adekunle Akinlade za su san makomarsu ranar Asabar

An kara bude reshen ma'ajiyar ne shekaru biyu da suka gabata bayan shekarun da yayi baya aiki.

Kara bude reshen matatar na daga cikin kokarin gwamnati na kawo sauki wajen lodi da rarraba man fetur.

Tsohon shugaban matatar na wancan lokacin, Maikanti Baru, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari na kokarin kawo hanyar saukake rarraba da samar da man fetur ga kowanne bangare na kamfanin.

Yace kara bude reshen da aka yi zai rage wahalhalun safarar man fetur daga Legas zuwa Ibadan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel