Kotun zaben Shugaban kasa: Muhimman hukunce-hukunce 7 da aka yanke zuwa yanzu

Kotun zaben Shugaban kasa: Muhimman hukunce-hukunce 7 da aka yanke zuwa yanzu

Kotun zaben Shugaban kasa na kan yanke hukunci a yanzu haka kan karar da jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da dan takararta, Atiku Abubakar suka shigar inda suke kalubalantar nasarar Shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben ranar 23 ga watan Fabrairu.

Kwamitin kotun zaben karkashin jagorancin Mohammed Garba na ta yanke hukunce-hukunce tun daga karfe 9:30 lokacin da aka fara shari’an.

1. Kotun zaben shgaban kasar ta yi watsi da ikirarin jam'iyyar PDP da Atiku na cewa shugaba Muhammadu Buhari ya yi amfani da yan sanda da sauran jami'an tsaro wajen magudin zabe.

2. Kotun zaben ta soke dukkan bukatar da hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta INEC ta gabatar na watsi da karar jam'iyyar PDP da Atiku Abubakar.

3. Kotun ta yi watsi da zargin cewa dan takaran kujeran shugaban kasa karkashin jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ba haifaffan dan Najeriya bane kuma bai cancanci takaran zabe ba.

4. Kotun ta soke wani jawabin shaidar da tsohon ministan jirgin sama, Osita Chidoka ya rubuta, domin goyon bayan karar Atiku Abubakar da PDP.

5. Kotun ta yi watsi da karar Atiku akan siyan kuri’u ta hanyar shirin mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo na Trader-Moni, cewa hakan bai da tasiri a zaben.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Atiku dan Najeriya ne, kotun zabe ta yanke hukunci

6. Kotun ta yi watsi da bukatar Buhari na cewa Atiku bai cancanci shigar da kara ba.

7. Kotu ta soke bukatar INEC akan lauyan Atiku, Livy Uzoukwu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel