Da dumi dumi: Jirgin farko na yan Najeriya ya dawo gida daga kasar Afirka ta kudu

Da dumi dumi: Jirgin farko na yan Najeriya ya dawo gida daga kasar Afirka ta kudu

Rukunin yan Najeriya na farko su 84 sun iso Najeriya daga kasar Afirka ta kudu, inda suka sauka filin sauka da tashin jirage na Murtala Mohammed dake jahar Legas, inji rahoton kamfanin dillancin labarum Najeriya.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito jami’an ma’aikatar kasashen waje ta Najeriya ne suka bayyana haka cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Laraba, 11 ga watan Satumba a garin Abuja, inda yace duk da cewa yan Najeriya 313 aka tabbatar za’a dauko, amma mutane 84 daga cikinsu kadai aka iya tantancewa.

KU KARANTA: Jirgin yakin Najeriya ya cilla bama bamai a motocin yakin Boko Haram

Ma’aikatar ta bayyana cewa yan Najeriya 640 ne suka bayyana niyarsa na dawowa Najeriya, kuma tuni suka yi rajista suna shirin tantancewa kafin a fara jigilarsu, ta kara da cewa rukuni na biyu za su dawo gida a ranar Juma’a.

“Ya kamata a ce jirgin Air Peace da zai dauko mutanen ya taso tun karfe 9 na safe, amma hakan bai yiwu ba saboda bincike da tsare tsare da jami’an hukumar shige da fice suka gudanarwa a kansu, haka zalika an samu tsaiko a na’urar kwamfuta, don haka mutan 84 kadai muka iya daukowa saboda duk mintin da jirgin ya kara a filin jirgi zai biya karin kudin fakin.” Inji shi.

Biyo bayan hare haren kyamatar baki bakaken fata ne shahararren dan kasuwan Najeriya kuma shugaban kamfanin Air Peace, Allen Onyeama ya dauki nauyin dauko duk wani dan Najeriya daya nuna sha’awar dawowa gida.

Tun a ranar 9 ga watan Satumba aka yi shirin fara jigilar yan Najeriyan, amma sakamakon yawancinsu basu da fasfon tafiye tafiye dole tasa aka dage zuwa ranar Laraba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel