Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban kasar Indonesia Jusuf Habibie ya rasu

Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban kasar Indonesia Jusuf Habibie ya rasu

Tsohon shugaban kasar Indoensia Bacharuddin Jusuf Habibie ya rasu a ranar Laraba bayan ya yi jinya a asibitin sojoji na Jakarta kan ciwon zuciya da ya ke fama da shi kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Habibie ya rasu yana da shekaru 83 a duniya.

Shugaban kasar Joko Widodo ta shaidawa manema labarai cewa, "A madadin mutane Idonesia da gwamnati ina mika sakon ta'aziyya ta kan rasuwar Farfesa BJ Habibie.

"Mr Habibie kwararren masanin kimiyya ne kuma shine jagoran kawo sauye-sauyen fasaha kuma shugaban Indonesia na uku."

DUBA WANNAN: Jam'iyyar PDP ba za ta sake yin tasiri a jihar Kaduna ba - Gwamna El-Rufai

A shekarar 2018, an kwantar da Habibie a asibitin Starnberg da ke kusa da Munich inda aka yi masa aiki kan wata cuta a zuciyarsa.

Habibie ya yi karatun Injiniya kuma ya yi aiki a kasar Jamus kafin daga bisani a 1976 ya dawo Indonesia domin bayar da gudunmawarsa ga fannin fasaha da a karkashin gwamnatin Shugaba Suharto.

Habibie ya shugabanci kasar daga watan Mayun 1998 zuwa Oktoban 1999.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel