Jana'iza: An dauko gawar Mugabezuwa kasar Zimbabwe

Jana'iza: An dauko gawar Mugabezuwa kasar Zimbabwe

A ranar Laraba ne aka dauko gawar tsohon shugaba, Robert Mugabe, zuwa kasar sa ta haihuwa, Zimbabwe, daga kasar Singapore, inda ya mutu.

An samu rabuwar kai a tsakanin mutanen kasar Zimababwe a kan mulkin marigayi Mugabe na tsawon shekaru 37, wanda aka bayyana shi a matsayin na kama karya da durkusar da tattalin arziki.

Jami'an tsaro a kasar Singapore sun yi komba domin rako gawar Mugabe zuwa filin jirgin sama domin dauko ta zuwa Zimbabwe.

Mugabe, tsohon dan gwagwarmaya, ya mutu ne ranar Juma'a yana da shekaru 95 a duniya.

Lafiyar tsohon shugaban kasar ta kara tabarbarewa ne bayan wani babban jami'in soja mai kusanci da shi ya jagoranci yi masa juyin mulki a shekarar 2017.

Ya mutu ne a Singapore, kasar da ya saba zuwa domin duba lafiyarsa. Gwamnatin kasar Zimbabwe ta aika wakilai karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Kembo Mohadi, zuwa kasar Singapore domin dauko gawar marigayi Mugabe zuwa gida.

Da safiyar ranar Laraba ne aka dauko gawar Mugabe inda aka rako ta zuwa filin jirgin sama bisa rakiyar jami'an tsaro.

Wani dan uwa ga tsohon shugaban kasar, Adam Molai, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasar Faransa (AFP) cewa jirgin da zai kawo gawar marigayi Mugabe zuwa Zimbabwe ya bar kasar Singapore ba tare da wani bata lokaci ba.

Ana iya jin karar tashin jirgin sama yayin da Molai ke fada wa AFP a wayar tarho cewa "yanzun nan jirgin mu ke barin filin jirgin sama a Singapore".

Ana sa ran shugaban kasar China, Xi Jinpin, tsohon shugaban kasar Cuba, Raul Castro, da dumbin sauran shugabannin kasashen Afrika zasu halarci jana'izar Mugabe, kamar yadda fadar shugaban kasar Zimbabwe ta bayyana.

Za a binne gawar Mugabe ranar Lahadi.

Jana'iza: Yadda aka karrama gawar Mugabe bayan isowar ta kasar Zimbabwe (Hotuna)

An dauko gawar Mugabe zuwa filin jirgin sama
Source: Twitter

Jana'iza: Yadda aka karrama gawar Mugabe bayan isowar ta kasar Zimbabwe (Hotuna)

Rakiyar gawar Mugabe zuwa filin jirgi
Source: Twitter

Jana'iza: An dauko gawar Mugabezuwa kasar Zimbabwe

Motar da ta dauko gawar Mugabe zuwa filin jirgi
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel