Da duminsa: An kubutar da mutane 7 da masu garkuwa da mutane suka sace a hanyar Abuja zuwa Kaduna (Hoto)

Da duminsa: An kubutar da mutane 7 da masu garkuwa da mutane suka sace a hanyar Abuja zuwa Kaduna (Hoto)

Jami'an rundunar tsaro na rundunar atisayen 'Thunder Strike' sun kubutar da matafiyan nan 'yan asalin garin Offa, jihar Kwara, da aka sace a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

An sace matafiyan ne ranar Lahadi da daddare.

Jami'an tsaron sun kubutar da su daga hannun masu garkuwa da mutane a garin Rijana dake yankin karamar hukumar Kachia a jihar Kaduna.

Kwamandan rundunar, Kanal Ibrahim Gambari, ne ya sanar da kubutar da mutanen yayin da yake nuna su ga manema labarai a wata makaranta dake garin Rijana.

"Mun samu bindigu samfurin AK47 guda biyu a wurinsu, kwanso mai alburusai guda biyar, wayoyin hannu guda biyu, kudi N100,000 da kakin soji guda uku," a cewarsa

Kanal Gambari ya bayyana cewa zasu damka mutanen da suka kubutar a hannun gwamnatin jihar Kaduna domin daukan mataki na gaba.

A cewarsa, akwai jami'an tsaro daga rundunar sojin sama, rundunar sojin ruwa, rundunar sojin kasa, jami'an 'yan sanda, DSS da NSCDC a cikin tawagar atisayen 'Thunder Strike'.

Babban makasudin kafa rundunar atisayen shine; domin ta yi yaki da kisan jama'a da kuma garkuwa da mutane a babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

DUBA WANNAN: Hanyar lafiya: Mabiya Shi'a a Kano sun yi zamansu a gidajensu

"Mun yi aiki ne da rahoton jami'an 'yan sanda a kan sace mutanen ranar Lahadi, mun shiga aiki tukuru domin ganin mun kubutar da mutanen, sun koma ga iyalansu. Mun rasa daya daga cikin masu bamu bayanai," a cewar Kanal Gambari.

Kwamandan ya bukaci matafiya da su guji yin tafiya da daddare a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna. Kazalika, ya ce idan tafiyar ta zama dole, to direba ya gaggauta juya wa idan ya hango shingen binciken ababen hawa.

Daya daga cikin mutanen da aka sace, Aisha Bisola, ta ce masu garkuwa da mutanen sun sace su ne ranar Lahadi da misalin karfe 9:30 na dare yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kaduna daga Kwara.

Ta bayyana cewa sun yi tafiyar kafa ta kusan sa'o'i uku kafin su karasa sansanin masu garkuwa da mutanen, wanda ke kan wani tsauni a cikin surkukin jeji.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa mutanen bakwai da aka sace sune; Bisola, Ahmad Abdulrafiu, Maryam Abubakar, Suleiman Kadoka, Lawal Temitope, Bala Abdullahi, da Abdulrazak Okunola.

Da duminsa: An kubutar da mutane 7 da masu garkuwa da mutane suka sace a hanyar Abuja zuwa Kaduna (Hoto)

Mutane 7 da masu garkuwa da mutane suka sace a hanyar Abuja zuwa Kaduna
Source: Twitter

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel