Kudin makaranta 'ya'yana ya sa na fara garkuwa da mutane

Kudin makaranta 'ya'yana ya sa na fara garkuwa da mutane

- Wani magidanci mai shekaru 30 ya bayyana cewa kudin makarantar yaransa yasa har ya fara garkuwa da mutane

- Magidancin mai 'ya'ya biyar dai na sana'ar kiwo ne

- Asirinsa ya tonu ne bayan da suka hada baki da 'yan kungiyarsu wajen garkuwa da wani mutumin da ya sani

Magidanci mai shekaru 30 a duniya ya bayyanawa hukumar 'yan sandan jihar Niger da manema labarai cewa ya fara garkuwa da mutane ne sanadiyyar rashin kudin makarantar yaransa biyar.

Wanda ake zargin kuma makiyayi, yace kiwon da yake yi ba ya samar masa da isasshen kudin da zai iya sauke nauyin da yake kansa.

"Abinda nake samu a kiwon dabbobi baya isa in biyawa yarana 5 kudin makaranta. Banda mataimaki; iyayena sun rasu tun ina yaro. A hakan ne na fara garkuwa da mutane," inji shi.

Da aka tambayesa ko matarsa ta san yana garkuwa da mutane?

Sai yace,"Matata ta san dai ni makiyayi ne amma bata san ina garkuwa da mutane ba, nasan ba za ta yafemin ba."

KU KARANTA: Kotun zabe: Gwamna Dapo Abiodun da Adekunle Akinlade za su san makomarsu ranar Asabar

Asirin wanda ake zargin ya tonu ne, bayan da aka yi garkuwa da wani Alhaji Yahaya Hamza na sansanin Fulani da ke karaye, jihar Kano a ranar 31 ga watan Augusta, 2019.

Hamza dai na kan hanyarsa ne ta zuwa Kano lokacin da ya hadu da wanda ake zargin har ya ba shi shawarar kwana a kauyen Ishau.

An gano cewa wanda ake zargin ya hada kai da wasu mutane biyu akan su yi garkuwa da Hamza tare da yi masa fashi.

Kungiyar tasu ta kira iyalan Hamza da bukatar kudin fansa har Naira miliyan 7 kafin su sakesa.

Jami'an 'yan sanda ne suka bi diddigi inda suka cafke wanda ake zargin a kauyen Ishau na jihar Niger.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, Muhammad Abubakar, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma yace wanda ake zargin ya amsa laifinsa tun kafin a gurfanar da shi gaban kuliya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel