Yanzu Yanzu: Kotu ta soke jawabin babban shaidan PDP da ke goyon bayan karar Atiku

Yanzu Yanzu: Kotu ta soke jawabin babban shaidan PDP da ke goyon bayan karar Atiku

Kotun zaben Shugaban kasa ta amince da bukatar Shugaban kasa Muhammadu Buhari na soke wani jawabin shaidar da tsohon ministan jirgin sama, Osita Chidoka ya rubuta, domin goyon bayan karar Atiku Abubakar da PDP.

Chidoka yayi aiki a matsayin jami’in tattara kuri’u na PDP a lokaci zaben Shugaban kasa sannan ya bayar da jawabi a matsayin babban shaida na mai kara.

A hukuncinta na hudu a yau Laraba, 11 ga watan Satumba, kotun tace jawabin na tattare da rashin kwarewa, duba ga cewar an ciketa ta yadda ta saba ma dokar zabe.

Kotun ta kuma soke wasu takardu da wasu bangarori da masu karar suka cike.

A baya dai Legit.ng ta rahoto cewa kotun zaben shugaban kasa dake zaune a Abuja za ta yanke hukunci yau Laraba, tsakanin shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Dukkan alkalan sun shiga kotun shari'a misalin karfe 9:28 na safe domin gabatar da hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel