Musaya: 'Yan bindigan Katsina sun sake sako mata 10 da suka yi garkuwa da su

Musaya: 'Yan bindigan Katsina sun sake sako mata 10 da suka yi garkuwa da su

'Yan bindiga da ke cikin dajin Ruga a daren ranar Talata sun sako mata 10 da jariri daya da suka yi garkuwa da su sakamakon sulhun da su keyi da gwamnatin jihar Katsina.

Kawo yanzu mutane 16 kenan 'yan bindigan suka saki sakamakon yarjejeniyar musayar da aka kulla tsakanin 'yan bindigan da gwamnatin jihar Katsina yayin da ake cigaba da tattaunawa na sulhu.

Sanawar ta Direktan Yadda Labarai na gwamnan jihar Katsina, Labaran Malumfashi ya fitar ya ce mata da jaririn da aka sako sun fita hayyacinsu kuma akwai alamun sun galabaita sosai.

Wakilin 'yan bindigan ne ka kawo su ofishin Gwamna Aminu Bello Masari misalin karfe 5.30 na yamma kamar yadda The Nation ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerar dan majalisar APC a jihar Kano

Sanarwar ta kara da cewa, "Nasarar da aka samu wurin musayar tsakanin 'yan bindiga da gwamnati na nuna nasarar da Gwamna Masari da takwarorinsa na jihohin Arewa maso Yamma ke samu domin kawo karshen ta'addanci, satar shanu da garkuwa da mutane da suka zama ruwan dare a Katsina, Zamfara da Sokoto.

"Sakin matan 10 da jaririn karo na biyu a rana guda ya nuna cewa bangarorin biyu da gaske su keyi kuma hakan zai nuna wa wadanda ke kyamar shirin cewa yarjejeniyar za ta kawo zaman lafiya."

Masari ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta cigaba da tattaunawar sulhu da 'yan bindigan inda ya bukaci su cigaba da cika alkawurran da suka dauka.

Ya ce, "Za zarar an kammala musayar wadanda aka kama, za a shiga mataki na biyu da uku na yarjejeniyar da zai mayar da hankali kan mika makamai da tubbabun 'yan bindigan za su yi."

Wadanda aka saki sun hada da Sa’adatu Garba, Dije Abdulmini, Dahara A. Garba, Salame Abu Musa, Rabi’atu Muazu, Shamsiyya Sabi’u from Fafara, Halima Hambali, Barira Adamu 'yan asalin kauyen Shifida sannan daga Manya A. Sani and Maryam Sani daga Garin mai wuya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel