Jam'iyyar PDP ba za ta sake yin tasiri a jihar Kaduna ba - Gwamna El-Rufai

Jam'iyyar PDP ba za ta sake yin tasiri a jihar Kaduna ba - Gwamna El-Rufai

- Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ce jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ba za ta sake tasiri a jihar ba

- Gwamnan ya yi ikirarin cewa jam'iyyar PDP ta shafe shekaru 16 tana mulkin jihar amma ba ta tsinana wani abin azo a gani ba

- Gwamna El-Rufai ya yi ikirarin cewa gwamnatocin PDP da suka gabata sunyi almubazarranci da kudin talakawa kuma sun raba wa abokansu filaye

Gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir Ahmed El-Rufai ya ce jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), ba za ta sake yin tasiri ba a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da ya ke jawabi ga magoya bayan jam'iyyar ta APC da suka kai masa ziyara domin taya shi murna kan nasarar da ya samu a kotun karrarakin zabe na jihar.

El-Rufai ya ce jam'iyyar ta PDP ta lalata jihar na tsawon shekaru 16 da su kayi suna mulki tare da almubazarranci da kudin talakawa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

El-Rufai ya ce, "A yau an ware tsakanin masu gaskiya da masu karya. Da izinin Allah, PDP ba za ta sake tasiri a jihar ba. Ba za muyi magana da yawa ba saboda idan Allah ya baka mulki, abinda ya dace kayi shine ka mayar da hankali kan aikin ka saboda Allah ya sawake maka ayyukan ka.

"Ba mu magana kan rashin adalcin da su kayi, ba mu magana kan kudin talakawa da suka banattar wurin gida gidaje kuma ba su gyra ruwa ba. Ba su samar da tittuna da kasuwanni ba.

"Kawai sun lalata garin da ya kamata ace sun gyra ne, sun raba wa abokansu filaye domin gina shaguna. Dukkan kudaden da aka basu na tsawon shekaru 16, ba za su iya nuna muku wani aiki da su kayi ba illa babban titin Kawo."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel