Xenophobia: Afirka ta Kudu ta fadi matakin da za ta dauka kan masu harin kiyayan bakar fata

Xenophobia: Afirka ta Kudu ta fadi matakin da za ta dauka kan masu harin kiyayan bakar fata

Kasar Afirka ta Kudu ta bullo da abinda ta kira tsari da gwamnati za tayi amfani da shi domin hukunta wadanda ke kai wa baki hari a kasar.

A ranar Talata, ministocin kasar uku sun ce tsarin ya hada da tattaro bayyanan sirri da zai taimakawa 'yan sanda wurin kama wadanda ke kai wa baki hari cikin gaggawa.

Ministocin da suka hada da na Shari'a, Kiyaye Laifuka da na Tsaro sun bayyana cewa gwamnatin kasar za ta kori duk mutanen da ke kasar ba tare da takardun izinin zama ba kamar yadda TVC News ta ruwaito.

Sun kuma ce gwamnatin za ta gurfanar da masu daukan aiki da ke saba dokar shige da fice na kasar.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerar dan majalisar APC a jihar Kano

Ministocin sun ce kawo yanzu an kama kimanin mutane 700 da ake zargi da hannu cikin hare-haren na kiyayan bakar fata tun ranar 1 ga watan Satumba.

Hare-haren ya janyo cece-kuce tsakanin mutanen sauran kasashen duniya musamman na Afirka.

Mutane da dama sunyi Allah-wadai da masu kai hare-haren inda suka bukaci gwamnatin kasar ta dauki matakin gaggawa domin magance matsalar.

Wasu mutanen a kafafen sada zumunta sun shawarci sauran kasashen Afirka su dauki matakin korar 'yan Afirka ta Kudu daga kasashen su har zuwa lokacin da kasar ta dauki mataki kan lamarin.

Tuni dai Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya bayar da umurnin fara dawo da 'yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu gida duk da cewa ba a tilastawa kowa dawowa ba.

Shugaba Buhari ya kuma tura tawaga ta musamman zuwa kasar ta Afirka Ta Kudu domin bin ba'asi kan afkuwar hare-haren na kiyayar bakar fata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel