Dalilin da ya sa na raba ma'aikatar makamashi, ayyuka da gidaje - Buhari

Dalilin da ya sa na raba ma'aikatar makamashi, ayyuka da gidaje - Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, ya bayyana dalilai da suka sanya ya yanke hukuncin raba ma'aikatar makamashi, ayyuka da gidaje, da kuma ma'aikatar sufuri da jiragen sama.

Shugaban kasar kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito ya bayyana cewa, inganta ayyuka da bunkasa harkokin su na gudanar ya sanya raba ma'aikatun inda kowanensu zai ci gaba da cin gashin kai wajen shimfida tsare-tsare masu nasaba da ci gaban kasa.

Shugaba Buhari ya jaddada cewa, mafi akasarin al'ummar kasar nan da suka kada masa kuri'u a yayin babban zaben kasa da ta tabbatar da nasarar sa, ta bayu ne da manufa ta samar da aminci da kuma inganta tsaro na tsare rayukansu da dukiya.

Haka zalika shugaban kasar ya ce al'ummar Najeriya sun sake tabbatar da nasararsa a yayin babban zaben kasa da aka gudanar a watan Fabrairun da ya gabata domin ci gaba da bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma inganta tubalin jagoranci wanda ya tsarkaka da rashawa.

KARANTA KUMA: Yadda za a shawarci mai tunanin kashe kansa

Jawaban shugaban kasar na zuwa ne a yayin zaman majalisar zartarwa na farko da ya jagoranta a zango na biyu na gwamnatinsa.

A yayin zaman majalisar da aka gudanar a babban dakin taro na Council Chambers da ke fadar Villa a birnin Abuja, shugaba Buhari ya kuma gargadi 'yan majalisar da su hada kai da juna wajen yin aiki tare domin cimma manufa daya.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel