Yadda za a shawarci mai tunanin kashe kansa

Yadda za a shawarci mai tunanin kashe kansa

Babu shakka mutum ya kashe kansa wata mummunar annoba da ta tunkaro bil Adama a wannan karni, inda a yanzu an yi kiyasin cewa cikin kowace dakika 40 mutum daya na rasa ransa ta hanyar kashe kai a fadin duniya.

A rahoton da jaridar BBC Hausa ta wallafa, alkalumma na nuni da cewa maza ne suka fi yawan debe wa kansu tsammani ta hanyar kashe kawunansu a duniya, inda mummunar annobar ta kai kaso 13.5 a cikin maza 100,000 idan an kwatanta da na mata 7.7 cikin mata 100,000 a shekarar 2016.

A yayin da babu wani rukuni ko kuma aji na mutane da wanann annoba ba ta ratsa cikin sun, walau mata, maza, yara ko kuma manya, aikata jakan ya sha bam-ban a tsakanin kasashen duniya.

KARANTA KUMA: Za a batar da cutar zazzabin cizon sauro a shekarar 2050 - WHO

Ga wasu muhimman shawarwari kan yadda za a jarraba shawo kan mai tunanin kashe kansa kamar yadda jaridar BBC Hausa ta wallafa:

1. A zabi wurin da babu hayaniya, inda mutumin zai iya sake wa da samun nutsuwa.

2. Tabbatar da cewa a kawai wadataccin lokacin ganawa da fuskantar juna wajen tattaunawa.

3. Idan wata magana mai sanya faduwar gaba ta gindayo a cikin tattaunawar ku, kada ku razana.

4. Debe kewa da daukar hankalin mutumin, sanya idanu cikin idanu wato a yi ido hudu da juna domin ba shi cikakken hankali.

5. Yin juriya da kuma hakuri domin bayar da amsa ko bayyana damuwarsa ka iya daukan lokaci.

6. A tabbatar da an yi amfani da budaddun tambayoyi wadanda ke bukatar amsoshi masu karin bayani sama da "eh ko a'a"

7. Kada ka katse shi ko ka kawo mafita; kada ka nuna cewa ka san yadda mutumin yake ji a ransa.

8. Ka bincika ko ya san inda zai samu taimakon likitoci.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel