Za a batar da cutar zazzabin cizon sauro a shekarar 2050 - WHO

Za a batar da cutar zazzabin cizon sauro a shekarar 2050 - WHO

Wani sabon rahoto da Muryar Duniya ta fitar na nuni da cewa, ana kyautata zaton za a iya kawo karshen cutar zazzabin cizon sauro wato Malaria a duniya a shekarar 2050.

Tawagar wasu kwarraru a fannin lafiya ta sha alwashin batar da wannan cuta daga doron kasa a shekarar 2050 muddin ta samu kyakkyawan hadin gwiwa daga hukumar lafiya ta reshen Majalisar Dinkin Duniya, WHO.

Duk da cewar wannan babban lamari ne da yiwuwarsa babu tabbas, kwararrun na lafiya na neman hadin gwiwar hukumar lafiya ta Duniya musamman a bangaren tanadar kudi masu tarin yawa domin batar da cutar Malaria.

Ya zuwa yanzu, alkalumma na nuni da cewa, akalla kimanin mutane miliyan 200 na kamuwa da cutar zazzabin cizon sauro, inda galibi ta ka murkushe kananan yara har lahira.

KARANTA KUMA: 'Yan daban daji sun sake kai hari jihar Neja

Muryar Duniya wato jaridar RFI Hausa mai tushe a kasar Faransa, ta ce akalla mutane miliyan 219 cutar Malaria ta kama cikin shekarar 2017 a duniya da adadi mai yawa a nahiyar Afrika inda kuma ta hallaka mutane dubu dari 4 da 35.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel