'Yan siyasa na gurgunta jami'o'in gwamnati a Najeriya - ASUU

'Yan siyasa na gurgunta jami'o'in gwamnati a Najeriya - ASUU

Kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU, ta zargi 'yan siyasa da gurgunta jami'o'in gwamnati a kasar ta hanyar shimfida tsare-tsare domin kare nartabar jami'o'in yan kasuwa da masu zaman kansu.

Zargin kungiyar na kunshe ne cikin wata sanarwa ta shugabanta, Farfesa Biodun Ogunyemi, lamarin da ya ce 'yan siyasa an ci gaba gurgunta jami'o'in gwamnati a kasar domin na 'yan kasuwa da na mazau zaman kansu su samu gindin zama.

Furucin Ogunyemi ya zo ne a yayin zantawa da manema labari bayan taron jiga-jigan kungiyar ASUU na kasa da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata cikin jami'ar tarayya ta nazarin noma da ke birnin Abeokuta a jihar Ogun.

Ya yi bayanin cewa, kungiyar yayin zaman majalisar zartarwa da ta gudanar, ta yanke shawarar watsi da sake kafa bankin ilimi na kasa.

Shugaban ASUU yake cewa, sake dawo da wannan tsari na bankin wata kitimurmura ce ta 'yan siyasar kasar nan da za ta ba su damar bai wa daliban jami'o'in 'yan kasuwa makudan kudi inda tuni suka zuba hannayen jari mai tsoka.

Haka zalika a yayin taron, kungiyar ASUU ta kirayi gwamnatin tarayyar Najeriya da ta gaggauta kaddamar da dokar ta baci kan harkokin ilimi a kasar nan.

Farfesa Ogunyemi ya bayyana damuwa dangane da gazawar gwamnatin tarayya a kan kaddamar da dokar ta baci kan harkokin ilimi kamar yadda ministan ilimi, Adamu Adamu ya zayyana a shekarar 2017.

KARANTA KUMA: Ta'addanci ya salwantar da rayukan fiye da mutane 1400 a Najeriya - Majalisar Dinkin Duniya

Har ila yau kungiyar na ci gaba da zargin gwamnatin Najeriya da jinkirin aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla tun a shekarar 2009 game da yadda za a inganta yanayin aiki a jami'o'i, da kuma rashin biyan mambobinta kudaden alawus da wasu sauran bukatu da ta cancanta.

Babu shakka kungiyar ASUU ta dade tana kai ruwa rana da gwamnati a kan bukatunta ne neman a inganta makamar aiki da kuma jami'o'i, lamarin da sau da dama ke haifar da yajin aiki masu hangen nesa ke hanin yana matukar yiwa karatu a jami'o'in kasar nan zagon kasa.

Baya ga haka kungiyar ASUU ta kirayi gwamnatin Najeriya da ta tashi ta farga domin magance matsaloli na rashin tsaro, tattalin arziki da kuma yaye kangin talauci da ya lullube al'ummar kasar nan, lamarin da ta ce ya sanya wasu da dama neman arziki da kuma tsira a wasu kasashen.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel