Ta'addanci ya salwantar da rayukan fiye da mutane 1400 a Najeriya - Majalisar Dinkin Duniya

Ta'addanci ya salwantar da rayukan fiye da mutane 1400 a Najeriya - Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talatar da ta gabata ta ce rayukan fiye da 'yan Najeriya 1,400 sun salwanta a sanadiyar ta'addancin masu garkuwa da mutane da kuma 'yan daban daji cikin watanni shida kacal a fadin kasar.

Daraktan Majalisar na Najeriya, Edward Kallon, shi ne ya bayyana hakan a birnin Makurdi na jihar Benuwe yayin ganawa da gwamna Samuel Ortom, lamarin da ya ce kashe-kashen makiyaya da 'yan daban daji ya sha gaban na kungiyar masu tayar da kayar baya ta Boko Haram.

Kamar yadda kafar watsa labarai ta Channels TV ta ruwaito, Mr Edward ya ce barazanar rashin tsaro a fadin kasar nan musamman a jihar Benuwe, inda rikicin makiyaya da manoma da kuma ta'addancin masu garkuwa da 'yan daban daji ya fi kamari ya fara wuce gona da iri a yanzu.

Babban jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana damuwa kwarai da aniya dangane kididdigar da gwamnatin Najeriya ta fitar, wadda ta tabbatar da cewa rayukan fiye da mutane 1,400 sun salwanta a sanadiyar ta'addancin masu garkuwa da kuma 'yan daban daji tun bayan babban zaben kasa kawo wa yanzu.

KARANTA KUMA: An kashe mana mambobi 15 yayin tattakin Ashura - IMN

A wani rahoton da jaridar Legit.ng ta ruwaito, hukumar jami'an tsaron cikin gida ta Najeriya NSCDC, a ranar Talata 10 ga watan Satumban 2019, ta cafke wani matashin dan acaba mai shekaru 20 kacal a duniya, Aliyu, da laifin cilla jaririnsa dan watanni hudu da haihuwa a cikin rafi.

Kwamadan hukumar NSCDC reshen jihar Neja, Mr George Edem, shi ne ya bayar da tabbacin wannan mummunan rahoto da cewar wanda ake zargi ya aikata laifin ne a kauyen Tamanine na karamar hukumar Borgu a jihar.

Sanarwa: Mun gode da kasancewarku tare damu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar ba mu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit.ng News

Online view pixel