Atiku vs Buhari: Muhimman Abubuwa 5 da Alkalai zasuyi amfani da su wajen yanke hukunci

Atiku vs Buhari: Muhimman Abubuwa 5 da Alkalai zasuyi amfani da su wajen yanke hukunci

Kotun zaben shugaban kasa dake zaune a Abuja za ta yanke hukunci yau tsakanin shugaba Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC da Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP.

Dukkan alkalan sun shiga kotun shari'a misalin karfe 9:28 na safe domin gabatar da hukunci.

Domin fahimtar masu bibiyanu, mun kawo muku abubuwa biyar da alkalan kotun zabe 5 karkashin jagorancin Alkali Mohammed Garba, zasuyi amfani wajen yanke hukunci:

1. Mai kuri'u mafi rinjaye: Kotun zaben za ta duba wanda ya samu kuri'u mafi rinjaye a fadin tarayya lokacin zaben. Atiku da PDP sunyi zargin cewa Buhari da APC sun tafka magudi kuma INEC ta kawar da kai.

2. Zargin magudi da rashawa: Atiku da PDP sun bayyanawa kotu zargin cewa hukumar yan sandan da Soji sun tafka magudi da rashawa a zaben kuma hakan ya sabawa ka'idojin kundin tsarin zaben Najeriya.

Kana, PDP da Atiku sun yi zargin cewa shirin TraderMoni da mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ke jagoranta, kokarin sayen kuri'un mutane ne.

KAI TSAYE: Komai ya kankama a kotun zaben shugaban kasa, Alkalai sun shigo kotu

3. Sabanin sakamakon zaben da aka sanar da wanda ke shaifn yanar gizon INEC: Atiku da INEC sun yi ikirarin cewa dubi ga sakamakon zaben da ke shafin yanar gizon INEC, sune masu kuri'u mafi rinjaye. Sabanin abinda shugaban hukumar ya sanarwa yan Najeriya.

4. Cancantan takarar zabe: Kotun za ta yanke hukumar kan shin shugaba Muhammadu Buhari da APC sun cika sharrudan sashe 131 na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ya bayyana cewa karatun sakandare na cikin sharrudan takara kujeran shugaban kasa kuma Buhari bai da kwalin karatun sakandare.

5. Zama dan kasa: Kotun za ta hukunci kan zargin da Buhari da APC sukayi na cewa Atiku bai cancanci yayi takara ba saboda ba haifaffen dan Najeriya bane.

An gabatar da hujjojin cewa garin Jada da aka haifi Atiku ba ta cikin Najeriya a shekarar 1946 da aka haifi Atiku. Garin Jada a lokacin na cikin kasar Kamaru.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel