An kama 'yan kungiyar Oro guda tara da suka kai wa musulmi hari a Ogun

An kama 'yan kungiyar Oro guda tara da suka kai wa musulmi hari a Ogun

Rundunar 'Yan sanda reshen jihar Ogun ta kama mambobin kungiyar Oro da aka ce sun kai hari kan musulmi a garin Idi-Iroko da ke karamar hukumar Ipoka na jihar Ogun a ranar bikin Oro.

The Nation ta ruwaito cewa 'yan kungiyar na Oro sun saka dokar hana fita ne a ranar Asabar a karamar hukumar amma al'ummar musulmi da ke garin suka saba dokar suka fita waje domin suyi sallah.

An ruwaito cewa 'yan kungiyar ta Oro sun fusata yayin da suka hango wasu musulmi da kirista a waje kuma suka far musu saboda rashin biyaya ga dokar hana fita a ranar bikin na Oro.

Majiyar Legit.ng ta gano cewa musulmi da kirista na garin sun fito yin harkokinsu ne a ranar duba da cewa wata babban kotu a jihar ta yanke hukunci na hana 'yan kungiyar na Oro yin bikin nasu da tsakar rana inda za su hana al'umma fitowa waje.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Kotu ta kwace kujerar dan majalisar APC a jihar Kano

Mr Tolahat Yahya, daya daga cikin wadanda aka kai wa harin ya yi ikirarin cewa 'yan kungiyar na Oro sun lalata masa mota yayin bikin.

Ya ce, "Muna dawowa daga wani taro ne a masallaci yayin da suka kai mana hari. Sun mana duka inda suka ce mun saba dokar hana fita da suka saka a ranar.

"Mun yi kokarin damke mutune uku cikinsu kuma muka mika su ga 'Yan sanda daga baya.

"Barazanar ya yi yawa, sun hana mu yin addinin mu duk da cewa anyi yarjejeniya cewa su dena yin bikin da tsakar rana."

Mai magana da yawun 'yan sanda na jihar, Abimbola Oyeyemi ya tabbatar da harin da aka kaiwa musulmin ya ce an kama wasu da ake zargi 'yan kungiyar na Oro ne.

Oyeyemi ya bayar da sunayen wadanda aka kama kamar haka, Desu, Monday Akinlolu, Dele Dada, Raimi Jacob, Dondo Sunday, Abiola Azeez, Olarenwaju Akerele, Nurudeen Lawal da Tetede Jamiu.

Mai magana da yawun 'yan sandan ya ce za a gurfanar da su gaban kotu kan laifin tayar da hankalin al'umma.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel